Matsin rayuwa ta sa wani dan siyasa ya rataye kansa

Matsin rayuwa ta sa wani dan siyasa ya rataye kansa

Wani mutum mai suna Gbemede K Bekegbo da yake zaune a unguwar Asignbi da ke Jihar Bayelsa, ya kashe kansa ta hanyar rataya sakamakon kuncin rayuwa da ya tsinci kansa a ciki.Bayelsa, ya kashe kansa ta hanyar rataya sakamakon kuncin rayuwa da ya tsinci kansa a ciki.

Dan siyasa ya rataye kansa

Dan siyasa ya rataye kansa

Marigayin mai kimanin shekaru 42, ya mutu ya bar ‘ya’ya bakwai da mace guda. Sai dai iyalan nasa sun ce Mista Gbemede bai bar wata takarda da za ta nuna takamaiman dalilin da ya sa shi kashe kansa ba.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Mutumin wanda tsohon Kansila ne, yanzu kuma yake aiki a Mazabar Ekeremor, ya rataye kan nasa ne a jiyar Alhamis da igiyar labuble a wani kango da yake kusa da gidansa.

KU KARANTA: Najeriya zata samu rangwamen kudin aikin Hajjin bana

Wata majiya daga wurin iyalansa ta bayyana cewar Mista Gbemede ya rataye kansa sakamakon rashin amincewa da matarsa ke nuna masa yayin mu’amalar aure. Sai dai wasu makusantansa sun ce, yana cikin matsananciyar damuwa ne, domin kusan wata bakwai ba a biya shi albashi ba, saboda suke ganin shi ne dalilin da ya sanya shi hakura da rayuwar duniya.

Wani makwabcin mamacin, Benjamin Samuel ya shaidawa majiyarmu cewar, sun kidima matuka da jin mutuwar Gbemede, domin sam ba su yi tsammanin zai aikata wannan abu ba.

Igiyar rataye mutum

Igiyar rataye mutum

“Muna tare da shi a daren Laraba, ‘ya’yansa sun kewaye shi, duk da na lura yana cikin damuwa saboda matarsa ba ta gida, na gan shi yana ta kokarin kiran ta a waya, amma bai same te ba.

“A wurina suka karbi hayar gidan da suke ciki, ban taba zato a ruyuwata makwabcina zai kashe kansa ba. Ina tsaka da bacci da jiyo ihun ‘ya’yansa da makwabta. Ina fitowa na ga abin da yake faruwa. Ni na yanke igiyar da ya rataye kan nasa, na yi kokarin ganin ko yana numfashi amma ina, tuni ya sheka barzahu.” In ji Samuel.

KU KARANTA: Wata sabuwar hayaniya ta balle a Ile-Ife

Wata mata da ta ce ‘yar uwa ce a wurin mamacin, ta ce “sam Gbemede ba ya fada mana matsalarsa. Duk da yana aiki, amma albashinsa ba wani na kirki ba ne, kuma bay a samuwa. Saboda haka nake zaton ya rataye kansa ne sakamakon damuwa da bacin rai.”

Kawunan makwabtan mamacin ya rabu gida biyu, inda wasu ke ganin matarsa ce ke azabtar da shi, yayin da wasu ke gani ita ce mai dauke da ragamar gidan, tana tallafa masa da ‘yar sana’ar da take yi ta sayar da Kalanzir.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma ga wani dan Najeriya yana yi wa yan siyasar mu kaca kaca

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel