'Ƙara-ƙara-ƙaka! Ahmadu Ali ya ƙaryata tsohon shugaban ƙasa IBB

'Ƙara-ƙara-ƙaka! Ahmadu Ali ya ƙaryata tsohon shugaban ƙasa IBB

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ahmadu Ali ya musanta maganan da tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida da yace wai sune shuwagabannin sashin sojojin jam’iyyar PDP.

Ahmadu ya musanta batun ne a ranar Alhamis, 30 ga watan Maris, yayin bikin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban hafsan soji Laftanar Janar Ishaya Bamaiyi mai taken ‘Vindication of a General’.

KU KARANTA: ‘Musabbabin rigima ta da gwamnan jihar Bauchi’ – Dogara

Ahmadu yace a tsawon shekaru ukun da yayi yana jagorantar jam’iyyar PDP, bai taba sanin wannan bangaren sojoji da IBB yace akwai ba, balle ma ace wai yana cikin su.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa IBB a satin daya gabata yana fadin “Mune shuwagabannin sashin sojin jam’iyyar PDP" yayin dayake karban bakoncin wata kwamitin sake fasalin PDP a karkashin jagorancin tsohon minista Farfesa Jerry Gana a gidansa dake Minna..

Janar IBB ya cigaba da fadin “Mune kwatankwacin sojojin kasar Ireland, amma na jam’iyyar PDP, nagode ma Allah daya bamu daman bullo da manufar PDP tayi mulkin Najeriya na tsawon shekaru 60.”

Dayake jawabi kan yadda EFCC ke tuhumar wasu tsoffin sojojin kasar nan kan badakalar satar kudade, Ahmadu Ali yace shi dai yasan tsofaffin sojoji kamar su Yakubu Gowon, Muhammadu Buhari sun sadaukar da rayukansu wajen bauta ma kasar nan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani mutum cikin fushi yayi kaca kaca da jam'iyyar APC

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel