Kungiyar matasan Arewa ta gargadi Yarbawa

Kungiyar matasan Arewa ta gargadi Yarbawa

Rahotanni sun kawo cewa kungiyar matasan Arewa, ta gargadi kungiyoyin Yarabawa a kudancin Najeriya har da kungiyar shugabannin ta wato Afenifere kan wasu kalamai da sukayi a kan rikicin kabilanci ya afku a tsakanin Hausawa da Yarabawa a Ile-Ife, jihar Osun.

Kungiyar matasan Arewa ta gargadi Yarbawa

Kungiyar matasan Arewa ta gargadi Yarbawa kan rikicin Ile-Ife

Karawar da akayi tsakanin al’umma Hausawa da kuma Yarabawa ‘yan asalin Ile-Ife a ranar 8 ga watan Maris yayi sanadiyar mutuwarmutane da dama, wanda kuma mafi aksarin su ‘yan arewa ne kuma yarbawan suka dinga furta munanan kalamai game da ‘yan Arewa shi yasa kungiyar ta matasan Arewa ta gargadan Yarbawa a kan haka.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya tura wasu sunaye Majalisa; ya za ayi ta wannan karo?

Shugaban kungiyar Alhaji Yerima Shettima ya bayyana cewa, “Muna jawo hankulan su da su bi a hankali domin kalamai da suke furtawa zai iya haddasa wata harin fansa.” Kungiyar arewacin na tunatar da kungiyar Afenifere da cewa su kiyaye, su bar haddasa fitina da rikici ta hanyar munanan kalaman su.

Alhaji Shettima, ya ce kalamai da ke fitowa daga kungiyoyin Yarabawan zai iya kawo cikas ga shari’a a kotuna da binciken da jami’an ‘yan sanda ke yi kan rikicin da kuma hukunta wadanda aka samu da laifin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon yadda Yarbawa suka kare Hausawa a lokacin rikicin Ile-Ife

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel