An sanya ma majalisar dattawa zafi kan Ndume

An sanya ma majalisar dattawa zafi kan Ndume

A jiya, Lauyoyi, kungiyoyin jama’a da sauran jama’a, sun tashi don kare Sanata Ali Ndume sannan kuma sun fada ma majalisar dattawa da ta janye hukuncin ta na dakatar da shin a tsawon watanni shidda.

An sanya ma majalisar dattawa zafi kan Ndume

Mutane da dama sun ga rashin dacewar hukuncin da majalisa ta dauka a kan Sanata Ali Ndume na dakatar da shi

Lauya mai kare hakkin dan adam Femi Falana (SAN) yace dakatar da Ndume, ya kasance saba ma doka a majalisar dattawa sannan ya bukaci sanatoci da su janye “kudirin da baya bisa doka.”

KU KARANTA KUMA: Buhari ya tura wasu sunaye Majalisa; ya za ayi ta wannan karo?

Da yake nuni bisa ga al’amarin Dino Melaye da sauran su da kuma majalisar wakilai, Falana a wata jawabi da yayi a jiya yace babban kotun tarayya ta kaddamar da dakatarwan mai karan a matsayin ba bisa doka ba sannan kuma ya saba ma kundin tsarin mulki kan cewa baza’a iya dakatar da dan majalisa sama da kwanaki 14 ba.

Har ila yau, Mista Taidi Jonathan, wani tsohon shugaban kungiyar Nigeria Bar Association (NBA), sashin Minna, a jiya ya bayyana cewa majalisar dattawa ta ketare iyakar ta kan hukuncin ta na dakatar da Sanata Ndume.

Jonathan ya fada ma hukumar dillancin labaran Najeriya (NAN) a Minna cewa: “Dakatar da sanata Ali Ndume ya fi karfin ikon yan majalisa a kundin tsarin mulkin jumhuriyyar Najeriya na 1999.

A cewar sa, sashi na 6 (6) (a) da (b) na kundin tsarin 1999 ta daura ikon hukunci ko cin tara a kan sashin shari’a sannan kuma kotu ce zata yanke hukunci.”

Haka kuma, mazauna jihar Borno sun nuna alhini kan al’amarin.

KU KARANTA KUMA: Anya wannan ne Buharin da aka sani kuwa- Inji wani Dan Majalisa

NAIJ.com ta samu labarin cewa wani Malam Musa Walama, mai narka karfe, ya bayyana cewa dakatarwan ya saba ma mulkin damokradiyya.

“Abun bakin ciki ne wannan al’amarin cewa majalisa ta yanke shawarar dakatar da shi kan ya tsaya a kan turban gaskiya. Wani irin sako sanatoci ke kokarin isar wa?” ya tambaya.

Malam Muhammad Asheikh, wani mai gadi, ya yi Allah wadai da dakatarwan, cewa an gukunta Ndume saboda ya fadi gaskiyar sa akan al’amarin kasa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli bidiyon yadda wasu ma'aikatan gwamnati ke zanga-zanga.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel