Majalisar Dattawa ta dakatar da Ndume don ya fadi gaskiya - Inji mazaunar Borno

Majalisar Dattawa ta dakatar da Ndume don ya fadi gaskiya - Inji mazaunar Borno

- Wasu mazaunar jihar Borno na kokawa kan dakatarwa da ‘yan majalisu suka yi wa tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa sanata Ali Ndume daga zauren majalisar.

- Mazauna sun bayyana cewa dakatar da sanatan abin takaici ne

Majalisar Dattawa ta dakatar da Ndume don ya fadi gaskiya - Inji mazaunar Borno

Majalisar Dattawa ta dakatar da sanata Ali Ndume saboda fadan gaskiya wanda ta shafi al'amurran kasar

Wasu mazaunar jihar Borno a ranar Alhamis, 30 ga watan Maris na kokawa kan dakatar da tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa sanata Ali Ndume na watanni 6 da shugabancin majalisar dattawan ta yi.

Mazauna sun bayyana cewa dakatar da sanatan abin takaici ne.

Malam Musa Walama, wani mai aikin karafuna ya bayyana cewa dakatar da sanata Ndume da majalisun ta yi ta bijire ga mulkin demokradiyya.

Ya ce matakin ya nuna cewa akwai damuwa game da jagorancin Majalisar Dattijan.

Wani mai aikin gadi malam Muhammad Asheikh, kuma ya yi Allah wadai da dakatarwar, yana mai cewa majalisar dattawar ta hukunta sanata Ndume saboda fadan gaskiya wanda ta shafi al'amurran kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon rikicin takardar shaidar sanata Dino Melaye

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel