Anya wannan ne Buharin da aka sani kuwa- Inji wani Dan Majalisa

Anya wannan ne Buharin da aka sani kuwa- Inji wani Dan Majalisa

Anya wannan ne Buharin da aka sani kuwa- Inji wani Dan Majalisa

Abubuwa ba su tafiya yadda ya kamata a Gwamnatin Buhari-Jibrin

Honarabul Abdulmumin Jibrin Dan Majalisar nan da aka kora kwanaki yace akwai matsala don kuwa ba wannan ne Muhammadu Buhari da kowa ya sani ba

Abdulmumin Jibrin mai wakiltar Kiru da Bebeji na Jihar Kano a Majalisar Wakilai ya dauki shafin sa na Twitter inda ya rika magana a game da sha’anin shugabancin Buhari kamar yadda NAIJ.com ta samu labari yace akwai fa matsala.

Hon. Jibrin ya yabawa Buhari kan abubuwa da dama irin su yaki da Boko Haram sai dai yace akwai inda shugaban ya nuna rauni da sakaci. Dan Majalisar yace yana mamaki ko shugaban kasar ya san abubuwan da ke faruwa ma a Najeriya.

KU KARANTA: 'Yan Majalisa sun takawa shugaban kasa burki

Anya wannan ne Buharin da aka sani kuwa- Inji wani Dan Majalisa

Honarabul Jibrin yace Anya wannan ne Buharin da aka sani a da

Abdulmumin Jibrin yake cewa anya wannan ne Sojan nan da aka sani a da wanda bai daukar wargi kuwa? Dan Majalisar ya karasa cewa watakila saboda rashin lafiyar shugaban ne ba a fada masa abubuwan da ke faruwa ko kuma wasu ke amfani da damar ta mugun nufi.

A jiya ma dai Majalisar Wakilai sun takawa shugaban kasa Muhammadu Buhari burki inda suka ce kara wa’adin wata Sakatare da yayi ya saba dokar tsarin mulkin kasa. A baya dai dama ana ta samun rikici da Majalisar Dattawa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani yayi kaca-kaca da Gwamnatin Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel