Jami’an yansanda sun ceto tsohon minista daga hannun masu garkuwa da mutane

Jami’an yansanda sun ceto tsohon minista daga hannun masu garkuwa da mutane

Tsohon ministan watsa labaru a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo Frank Nweke Junior daga hannun barayin mutane masu garkuwa.

Jami’an yansanda sun ceto tsohon minista daga hannun masu garkuwa da mutane

Frank Nweke

NAIJ.com ta samo rahoton yansanda masu aiki akan titin Kaduna zuwa Abuja ne suka ceto tsohon ministan a ranar Alhamis 30 ga watan Maris.

KU KARANTA: ‘Musabbabin rigima ta da gwamnan jihar Bauchi’ – Dogara

Tsohon minista Frank ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter inda ya gode ma jami’an rundunar yansanda da suka kawo masa daukin gaggawa a lokacin da yake da tsananin bukatarsu. Sa’annan ya yaba musu da yadda suke tsaron al’ummar kasa.

Jami’an yansanda sun ceto tsohon minista daga hannun masu garkuwa da mutane

Frank Nweke tare da yansandan da suka cece shi

“Yan Najeriya mutanen kirki, yansanda sun kawo min agaji akan titin Kaduna zuwa Abuja, Allah ya saka ma jami’an tsaron mu da alheri.” Kamar yadda Nweke ya rubuta a shafinsa na Tuwita.

Sakamakon rufe tashar tashi da saukan jiragen sama dake Abuja da karkatar da jiragen zuwa jihar Kaduna yasa gwamnati ta karfafa tsaro akan titin Kaduna zuwa Abuja don tabbatar da tsaron mutane da dukiyoyinsu musamman matafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Minista Amaechi yace a kullum yana sauraron ra'ayin yan Najeriya, kalli bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel