Majalisa tayi wa dokar tsarin zabe garambawul

Majalisa tayi wa dokar tsarin zabe garambawul

A zaman Majalisa Sanatoci sun amince ayi amfani da na’urar tantace masu zabe watau ‘Card Reader’ a zabe mai zuwa wanda wannan babban cigaba ne aka samu

Majalisa tayi wa dokar tsarin zabe garambawul

Majalisa tayi na'am da na'urar card reader

A jiya ne Majalisar Dattawa ta amince da ayi amfani da na’urar tantace masu zabe wanda aka sani da turanci a matsayin Smart Card Reader. Majalisar tayi wa tsarin zaben kasar na 2010 garambawul domin gyara harkar zabe.

Shugaban Majalisar Bukola Saraki ya jagoranci zaman inda ya kuma tabbatar da wannan kudiri. Sanatocin kasar dai sun yi garambawul ne ga sashen na 52 na dokar tsarin zabe na kasar inda ta ba Hukamar INEC damar amfani da na’urori na zamani wajen gudanar da zaben.

KU KARANTA: Ana muhawara game da tsarin zabe a Majalisa

Majalisa tayi wa dokar tsarin zabe garambawul

Shugaban Hukumar INEC na kasa

Majalisar ta dai kawo garambawul da dama a harkar zabe daga cikin an tsaida kudin fom din takarar shugaban kasa da sauran masu takara. Majalisar ta kuma ragewa Gwamnoni karfi wajen zaben masu fitar da gwani a zaben farko.

Kwanaki ne NAIJ.com ta kawo maku rahoto cewa Hukumar INEC tace a zabe mai zuwa na’ura za ayi aiki da su a maimakon a rika tura sako da hannu daga dakin zabe zuwa dakin zabe. INEC tace za a samu cigaba tun da za a rika aiki da na’uran zamani har wajen rage magudi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nayi da na sanin zaben APC inji wani mutumi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel