Gwamnatin jihar Legas ta karrama Tinubu (Hotuna)

Gwamnatin jihar Legas ta karrama Tinubu (Hotuna)

Kimanin sati biyu kenan da gwamnatin jihar Borno a karkashin jagorancin gwamna Kashim Shettima ta karrama jagoran jam’iyyar APC Ahmed Bola Tinubu, inda ta sanya sunansa a wasu rukunin gidaje, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito a baya.

Gwamnatin jihar Legas ta karrama Tinubu (Hotuna)

Bola Tinubu

Ita ma gwamnatin jihar Legas ta bi sawun takwaranta jihar Borno inda ta karrama Tinubu a daidai lokacin dayake bikin cikar sa shekaru 65 a duniya.

KU KARANTA: Hukumar kwastam ta canza ma manyan jami’anta 337 wuraren aiki

Gwamnan jihar Legas Akinwumi Ambode ya rada ma wata katafariyar gada daya gina suna gadar Ahmed Bola Tinubu, sa’annan ya bayyana wani mutum mutumi da aka gina na fuskar ubangidan nasa.

Gwamnatin jihar Legas ta karrama Tinubu (Hotuna)

Mutum mutumin Tinubu

Jagora Tinubu da kansa ya kaddamar da gadar tare da mutum mutumin dake karamar hukumar Alimisho, inda ya samu rakiyar gwamnan jihar Ambode, tare da Uwargidarsa Oluremi Tinubu da sauran manyan jami’an gwamnatin jihar.

Gwamnatin jihar Legas ta karrama Tinubu (Hotuna)

Gadar Tinubu

Daga karshe Tinubu ya gode ma gwamna Ambode, sa’annan ya yaba da kokarin dayake yi musamman wajen cika alkawurran daya daukan ma al’ummar jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani yaro ya zana manyan mutane, cikinsu har da Tinubu, kalli bidiyon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel