Allah wadarar naka ya lalace, miji yayiwa yar matarsa fyade

Allah wadarar naka ya lalace, miji yayiwa yar matarsa fyade

Wani mutum mai shekaru 55 mai suna, Magaji Dansale, yayiwa yarinya mai watanni 7 da haihuwa fyade a kauyen Marmachi, karamar hukumar Musawa a jihar Katsina

Wani dan jihar Katsina yayiwa jaririyar watanni bakwai da haihuwa fyade

Wani dan jihar Katsina yayiwa jaririyar watanni bakwai da haihuwa fyade

Mahaifiyar yarinyar Zeenatu Muntari, ta bayyanawa manema labarai cewa ta rabu da mahaifin yarinyan ne ta auri Dansale.

NAIJ.com ta ruwaito mahaifiyar tana mai cewa tana zargin ta sha wani abun da ya sata ta kwashe awanni tana bacci har ya samu damar yin lalatan da yayi.

KU KARANTA: Buhari zai koma Landan - Garba Shehu

Game da cewarta ta tashi daga barci domin baiwa yarinyan nono sai taga jini a farjin jaririyar.

“Da na fadawa mijina sai ya fara kuka; yace wasu zasu fara tuhumarshi. Da gari ya waye, yayinda nike wanki, sai naga jini a wandonsa.

“Daga baya sai yaje daji ya kawo min ganye in bata, wai basir ne. daga baya muka kai yarinyar asibitin Malumfashi inda likita ya tabbatar da cewa fyade ne kuma an sanar da yan sanda.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel