An dakatar da shugabannin makaratun firamare 9 a wannan jihar (Dalili)

An dakatar da shugabannin makaratun firamare 9 a wannan jihar (Dalili)

Biyo bayan zanga-zangar lumana da dalibai tare da malaman makarantun firamare na jihar Taraba suka gudunar don neman a biyasu albashinsu na kusan watanni takwas, yanzu haka gwamnatin jihar Taraba ta rubuta takardar dakatar da wasu shugabanin makarantun firamare a jihar.

Daliban makaranta

Daliban makaranta

Kamar yadda bayanai ke nunawa gwamnan jihar Taraban Akitet Darius Dickson Isiyaku, ne ya baiwa shugaban Hukumar Kula Da Makarantun Firamari Na Jihar Taraba, umarnin dakatar da shugabanin makarantun firamare tara wato suspension ,dake fadar jihar sakamakon zanga-zangar lumana da dalibai tare da malamansu suka gudunar don neman a biyasu albashinsu na kusan watanni takwas.

NAIJ.com dai ta samu labarin cewa a wata takardar umarni daga hukumar ilimin bai daya da aka aikewa sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar 16, an bayyana cewa an dau wannan mataki ne sakamakon zanga-zangar lumana da daliban makarantun firamare da kuma malaman suka yi, wanda hakan ya sabawa doka.

KU KARANTA: Yan majalisa sunce ba zasu yadda ayi anfani da katin zabe ba

Hon.Semon Audu Galadima, dake cikin kwamishinonin hukumar kula da makarantun firamare na jihar yace dole gwamnati ta dau wannan mataki.

Tuni wannan batu ya soma jawo cece-kuce, inda wasu malaman ke cewa ai tura ce ta soma kaiwa ga bango, da hakan yasa Malaman da kuma daliban makarantun firamaren nuna fushinsu.

Barr.M.B Mustafa na cikin lauyoyin da ke kai gwauro da mari don ganin an biya Malaman hakkokinsu yace da ban mamaki wannan mataki da gwamnatin jihar ke shirin dauka a yanzu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli yadda wasu ma'aikatan gwamnati suke zanga-zanga

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel