An kara samun wani Dan Majalisa da takardun bogi

An kara samun wani Dan Majalisa da takardun bogi

Kwanaki aka yi ta takaddama inda aka zargi Sanata Dino Melaye da cewa bai kammala Digirin sa ba a Jami’a. Yanzu haka an kara samun wani Dan Majalisa a cikin wannan matsala

An kara samun wani Dan Majalisa da takardun bogi

An damke wani Dan Majalisa mai takardun bogi

Ana zargin wani Dan Majalisar Wakilai da cewa bai da takardun shaidar karatu. Dan Majalisar Wakilan Honarabul Nse Ekpenyong mai wakiltar Jihar Akwa-Ibom ya bayyana a gaban kotu a Birnin Awka dazu kamar yadda NAIJ.com ta samu labari.

Hukumar EFCC mai yaki da zamba ne dai ta damke wannan Dan Majalisa mai takardun bogi. Ana zargin cewa Honarabul Ekpenyong ya kirkiri takardar shaidar Diploma ta karya ne daga kwalejin karatu na Jihar Abia.

KU KARANTA: Tofa: Za a rufe Jam'o'in Najeriya

An kara samun wani Dan Majalisa da takardun bogi

Tir: An damke wani Dan Majalisa da takardun bogi

Honarabul din dai ya bayyanawa kotu cewa yana da gaskiya inda Lauyan sa Emmanuel Isangedoho ya nemi a bada beli amma EFCC ta ci damara tace sam ba za ayi haka ba. Alkali Ijeoma Ojukwu ya bada belin daga karshe inda yace shari’ar ba za ta dade ba.

A game da rikicin da ake bugawa da Majalisar yanzu haka shugaban kasa ya nada kwamiti da za ta zauna da Sanatoci domin kawo karshen takaddamar. Mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo ne zai jagoranci wannan kwamiti domin sulhu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sanata Dino Melaye bai da satifiket

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel