Buhari ka taimaka ka sa ido kan Gwamnoni - Wani shahararren dan siyasa

Buhari ka taimaka ka sa ido kan Gwamnoni - Wani shahararren dan siyasa

- Kimanin Naira miliyan dubu dari biyar ne gwamnatin Buhari ta ba ma jihohi domin biyan wasu bukatunsu to sai dai wai an soma gano wasu cikin kudaden a wuraren da ba su kamata ba

- A kokarin da yayi na fadakar da mutane akan yadda gwamnatinsa ke kashe kudi, gwamnan jihar Adamawa Alhaji Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla yace lokacin da ya karbi mulki babu hanyoyi a jihar saboda haka dole ne ya mayar da hankali akan ginasu domin a samu cigaba

Buhari da wasu siyasa

Buhari da wasu siyasa

A cewarsa idan ba'a gina hanyoyi ba tare da wasu abubuwa babu cigaba kuma masu saka jari ba ma zasu yi tunanen jihar ba balantana har su nemi saka jari. Idan kuma babu masu saka jari ba za'a kirkiro ma matasa ayyukan yi ba. Yace sun karbi mulki ne domin su yiwa wadanda suka zabesu aiki ba su cimma muradun kansu ba.

To saidai duk ikirarin da gwamnonin keyi na yiwa mutanensu aiki da kudin da gwamnatin tarayya ta basu akwai wadanda suke ganin ba haka batun yake ba.

KU KARANTA: Ina masallaci lokacin da aka tsige ni - Ndume

NAIJ.com dai ta samu labarin cewa Onarebul Abdullahi Terembe tsohon kwamishsnan yada labarai a jihar Adamawa yana ganin akwai bukatar Shugaba Buhari ya binciki gwamnoni akan yadda suka kashe kudin Paris Club da ya raba masu.

Yana mai cewa har yanzu "bani da kwarin gwuiwa zasu yi anfani dashi ta wannan wurin saboda kudaden da aka basu a can baya akwai wasunsu da basu yi anfani dasu ba ta hanyar da ta dace".

Inji Terembe tunda ba'a yiwa gwamnonin wani hukumci ba yanzu ma idan sun samu wani sabon kaso zasu yi anfani dashi ne yadda suka ga dama saboda bisa ga shari'a suna da kariya, ba'a isa a tursasasu ba. Dalili ke nan da wasunsu ke maganganun da suka ga dama akan kudaden. Yace yawancin gwamnonin sun zo kasuwanci ne.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ga kuma labarin wasu masu bautar kasa nan suna taimakon al'umma

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel