Allah Sarki! ka ga yadda mutanen nan suka kashe Abdulhakeem Bauchin Bauchi mai 'blog'

Allah Sarki! ka ga yadda mutanen nan suka kashe Abdulhakeem Bauchin Bauchi mai 'blog'

- Ana kan bincike maganan domin a sani ainihin muradi da yasa suka yi wannan

- Idan an lura, za a gan cewa dukkan lamuran, har wanda ya shafe Abdulhakeem Bauchin Bauchi

- Za a cajin su zuwa kotu akan laifin hada baki, domin aikata kisan kai da fashi da makami

Ga idanu wanda sun kashe Abdulhakeem Bauchin Bauchi

Ga idanu wanda sun kashe Abdulhakeem Bauchin Bauchi

A ranar 12 ga watan Maris game da karfe 5:00 na safe, shi ne wasu suka kashe Abdulhakeem Bauchin Bauchi. Ba’a gan gawan sa sai bayan kwana 5. An gano gawan a Rugun Jira dutse ta wajen Gwallameji a Jihar Bauchi ranar 17 ga watan Maris.

Binciken yan sanda, haɗe da ‘yan kame-kamen masu garkuwa da mutane a kwamand na Bauchi shi ne ya kawo yadda aka kama su.

Ga sunaye daga cikin wadannan da ake zargin sun aikata mugun aikin:Michael Sansai, shekaru 23 na Rafin Zurfi Yelwa, Sama'ila Uzima, shekaru 24 na Yelwa (mai karɓar), William Yakubu, shekaru 28 na dayan adireshin, Dauda Akanni 26 na Yelwa.

KU KARANTA: An aika wasu mutane gidan yari a dalilin lalata da maza a Kano

Bincike na farko ya bayyana cewa, Michael Sansai, na daya daga cikin ‘yan daban ‘Black Axe Confraternity.’

Ga abubuwar da aka tararda gare su: Wani bakin Nokia 225 na marigayin, dunkulin ganye 7 na ‘yan zargin, kaya da margayin ya sa ranar da aka kashe shi, ‘sim card’ da sauran abubuwa.

Ana kan bincike maganan domin a sani ainihin muradi da yasa suka yi wannan. ‘Yan sanda na kuma kan ƙoƙarin gane sauran da sun gudu. Sannan, za a cajin su zuwa kotu akan laifin hada baki, domin aikata kisan kai da fashi da makami.

Haka kuma wasu: Yusuf Ibrahim Babangida, Shedrack Ayuba, Samsu Saidu, Hassan Umaru Hussaini suka hada baki game da karfe 11; 05 na safe, kashe wani Abubakar Adamu mai shekaru 28 na Alkaleri karamar hukumar jihar Bauchi a Unguwan Kuji a Yelwa, bayan da suka jefar da gawarsa a Rugun Jira Dutse.

KU KARANTA: Yadda wata jaririya ta sha da kyar bayan an binne ta da ranta a cikin bola (Hotuna/bidiyo)

Bisa ga lafazin rahoton 'yan sanda, bincike ya nuna cewar, an kama su kuma da waya (Nokia 220) na marigayin, tabarya da jinni, wuka da jinni da kuma sauran abubuwa.

Yadda NAIJ.com ya samu rahoton, abin damuwan mutane shi ne, idan an lura, za a gan cewa dukkan lamuran, har wanda ya shafe Abdulhakeem Bauchin Bauchi, duk an aikata ne a gidan Sarkin Kuji wani mai sunan Adamu Mohammed, mai shekaru 57 na Kusu a Yelwa, wanda aka kama, kuma yana kan taimako 'yan sanda a gudanar da bincike. Bincike ya kara bayyana cewa duka 2 (marigayi) ne aka jefar a cikin wannan wuri a ta yanayi daya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan bidiyo na nuna wani vulcaniser da aka ce ya mutu amma bai mutu ba

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel