Hukumar kwastam ta canza ma manyan jami’anta 337 wuraren aiki

Hukumar kwastam ta canza ma manyan jami’anta 337 wuraren aiki

A kokarinsa na sake fasalin hukumar kwastam, shugaban hukumar Kanal Hamid Ali mai ritaya ya amince da sauya ma wasu manyan jami’an hukumar kwastam masu mukamin mataimakan kwantrola wuraren aiki.

Hukumar kwastam ta canza ma manyan jami’anta 337 wuraren aiki

Shugaban hukumar kwastam Hameed Ali

Hamid Ali ya sauya ma jami’an wuraren ayyukan ne inda ya rarrabasu dukkanin ofisoshin hukumar kwastam dake fadin kasar nan, kuma ya umarce su dasu koma inda aka sauya musu na tare da bata lokaci ba.

KU KARANTA: Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU na shirin shiga yajin aikin gama gari

Mataimakin kaakakin hukuma ta kwastam Abubakar Dalhatu ne ya sanar da sauyin cikin wata sanarwa daya fitar a Abuja a ranar Laraba 29 ga watan Maris, inda yace sauyin ya fara aiki nan take.

Sakamakon sauyin da aka samu a hukumar, an nada Joseph Attah a matsayin jami’in sadarwar hukumar, yayin da aka mayar da Babadidi B daga FOU zuwa tashar Apapa dake Legas, sai kuma Udenze da amayar da shi zuwa TCIP daga sashin kimiyyar hukumar, shi kuma Ilesanmi ya koma yankin Kaduna da Katsina, da dai sauransu.

Kamar yadda NAIJ.com ta samo rahoto, shugaban hukumar kwastam Hamid Ali ya bukaci jami’an da sauyin ya shafa dasu baiwa shugabannin ofisoshin da aka mayar dasu goyon bayan data dace, don tabbatar da ingantaccen aiki da gudanar da ayyuka cikin gaskiya da rikon amana.

“A wannan lokacin jama’a na sa ido don ganin muna samar ma kasar isashshen kudade, tare da tabbatar da tsaron kasar, don haka ba zamu yi kasa a gwiwa ba.” Inji Hamid

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga wani bidiyo inda yan Najeriya ke tofa albarkacin bakinsu kan farashin kayan abinci

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel