Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU na shirin shiga yajin aikin gama gari

Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU na shirin shiga yajin aikin gama gari

Kungiyar malaman jami’o’in kasar nan, ASUU tayi mi’ara koma baya kan alkawari data dauka na cewa ba zata sake shiga yajin aiki ba, inda aka jiyo kururuwarta tana barazana shiga sabon yajin aikin gama gari.

Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU na shirin shiga yajin aikin gama gari

Shuwagabannin ASUU

ASUU tayi barazanar shiga yajin aikin ne a watan Yulio muddin gwamnati ta gagara biyan malaman jami’o’in kasar nan bashin alawu alawus da suke bi daya tasar ma naira biliyan 128.

Shugaban ASUU na kasa, Biodun Ogunyemi ne yayi wannan barazana a wata zantawa da yayi da manema labaru a jami’ar Abuja ranar Laraba 29 ga watan Maris, inda yace malaman jami’a a Najeriya suna bin gwamnatin tarayya bashin naira biliyan 128, kamar yadda NAIJ.com ta samo rahoto.

KU KARANTA: Buhari ya gayyato likitocinsa Najeriya, ya fasa komawa Asibitin Landan

Shugaban yace “Sakamakon gazawa daga sashin gwamnati na biyan mu bashin da muke binta akan tsarin da muka shirya, don haka kwamitin koli na kungiyar ASUU ta yanke shawarar gwamnati ta biya dukkanin basussukan da malamai ke binta zuwa watan Yulio na 2017.”

Shugaban ya kara da cewa gwamnati na jinkirin sakin lasisin kamfanin kula da fanshon ma’aikatan jami’a, duk da cewa kamfanin ya cimma dukkanin wasu sharudda da ake bukata daga wajensa, inda yace rashin bada lasisin kamfanin ya sanya ya karya kwarin gwiwar ma’aikatan da suka ajiye aiki.

Bugu da kari shugaban ya bayyana rashin sakin yarjejeniyar fahimtar juna da ake tsakanin ASUU da gwamnati a shekarar 2013 na sake inganta jami’o’in gwamnati na kawo cikas ga gudanawar jami’o’in kasar nan.

“Yarjejeniyar ta tabbatar da cewa za’a sakar ma jami’o’in Najeriya naira biliyan 200 a shekarar 2013 don inganta su kamar sauran sa’o’insu dake fadin duniya. Daga nan kuma za’a cigaba das akin naira biliyan 220 har na tsawon shekaru 5, jimillai dai naira triliyan 1.3 zuwa shekarar 2018. Amma har yanzu ko sisi ba sakar ma jami’o’in ba.” Inji Ogunyemi

Don haka ne kungiyar take sanar da gwamnati matakin data dauka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon zanga zanga da mata suka yi ma gwamnati kan rashin biyan bukatunsu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel