‘Auratayya shine sahihin hanyar magance rikicin Fulani makiyaya da manoma’ – Fasto Zuga

‘Auratayya shine sahihin hanyar magance rikicin Fulani makiyaya da manoma’ – Fasto Zuga

Wani limamin coci mai suna Fasto Sam Zuga ya dauki hanyar magance rikici da tashin hankali dake yawan faruwa tsakanin manoma da Fulani makiyaya a jihar Binuwe.

‘Auratayya shine sahihin hanyar magance rikicin Fulani makiyaya da manoma’ – Fasto Zuga

Fasto Zuga

NAIJ.com ya samo rahoton fasto Zuga ya bada nasa gudunmuwar wajen kawo karshen rikice rikice da kiyayya dake tsakanin kabilun guda biyu wanda yayi sanadiyyar rasa rayuwka da asarar dukiyoyi da dama.

KU KARANTA: Buhari ya gayyato likitocinsa Najeriya, ya fasa komawa Asibitin Landan

Kamar yadda Fasto Zuga ya nuna a shafinsa na Facebook, yace auratayya ne kadai hanyar da zata kawo zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma yan kabilar Tiv a jihar Binuwe, inda har ya daura ma wasu ma’aurata aure.

A hotunna da faston ya daura a shafin nasa, ya nuna auren daya daura tsakanin wata bafulatana da mijinta dan kabilar Tiv, kuma manomi. Faston yace yana da tabbacin samun yawan auratayya tsakanin makiyaya Fulani da manoma ne kadai hanyar magance kiyayyan dake tsakaninsu, inda da gaske ake wajen kawo karshen rikicinsu.

Faston yayi ma hotunnan taken “Dabarar kawo karshen yake yake tsakanin Fulani da Tiv shine kamar yadda muka daura ma wata bafulatana aure da mijin tad an kabilar Tiv a garin samzuga a ranar 28 ga watan Maris”

Ga sauran hotunan bikin nan:

‘Auratayya shine sahihin hanyar magance rikicin Fulani makiyaya da manoma’ – Fasto Zuga

Fasto Zuga tare da ma'auratan

‘Auratayya shine sahihin hanyar magance rikicin Fulani makiyaya da manoma’ – Fasto Zuga

Amarya da Ango

‘Auratayya shine sahihin hanyar magance rikicin Fulani makiyaya da manoma’ – Fasto Zuga

Amarya na baiwa Ango nono

Ku biyo anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon halin da rikicin manoma da makiyaya ya jefa jama'an kudancin Kaduna

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel