An haɗa Ali Nuhu, Maryam da Rahama Sadau cikin fim ɗin ‘Hakkunde’

An haɗa Ali Nuhu, Maryam da Rahama Sadau cikin fim ɗin ‘Hakkunde’

Wani kayataccen fim dake kan hanyar fitowa mai suna ‘Hakkunde’ ya tara jarumai da dama wadanda zasu fadakar da masu kallo kan matsaloli daban daban tare da nishadantar dasu.

An haɗa Ali Nuhu, Maryam da Rahama Sadau cikin fim ɗin ‘Hakkunde’

Ali Nuhu da Rahama Sadau

Fim din ‘Hakkunde’ shiri ne wanda zai bada labarin wani matashi daya kammala karatunsa na digiri, sai dai rayuwa ta juya mai baya, inda ya sha fama a lamurran soyayya, danginsa, nuna kiyayya, rashin tsaro, al’adar gargajiya daga bisani ya koma shaye shaye.

KU KARANTA: ‘Ban ga dalilin taƙaddama tsakanin Sanatoci da Hamid Ali ba’ – Inji Dogara

‘Hakkunde’ ya bibiye rayuwar wannan matashi tun daga fadi tashin da yayi fama dashi a rayuwwarsa har zuwa lokacin daya samu nasara.

An haɗa Ali Nuhu, Maryam da Rahama Sadau cikin fim ɗin ‘Hakkunde’

Maryam Booth

Mashiryin shirin shine Asurf Oluseyi, kuma tuni an saki wani sashi na fim din Hakkunde don dandana ma yan kallo dadin fim din.

Wasu daga cikin jaruman dake cikin ‘Hakkunde’ sun hada da Frank Donga, Ali Nuhu, Maryam Booth, Ibrahim Daddy, Isa Bello J, Rahama Sadau da Hadiza Soja, kuma an dauki fim din a garuruwan Kaduna da jihar Legas. Shahararren marubuta kamar su Oluseyi, Tomi Adesina da Gift Imafidon ne suka shirya shirin.

Labarin fim din ‘Hakkunde’ ya bi salon rayuwar jama’a nay au da kullum, matsalolinsa, da yadda suke tafiyar dasu, sai dai a wannan karo, Hakkunde ya mayar da hankali kan wani matashi mai suna Akande da yayi fama wajen neman aiki don samun ingantaccen rayuwa.

Mashiryin shirin, Oluseyi Asurf yace “Fim din na bayanin rayuwar dan Najeriya matashi wanda ya kammala digiri, da yadda ya sha bakar wahala wajen neman aiki don samun ingataccen rayuwa. Fim din yana fadakar da matasa dasu fahimci rayuwa yadda ta canza a yanzu, musamman yadda tattalin arziki yayi kasa, don su yi amfani da canjin da rayuwar tazo da shi wajen cigaban kansu.”

Kamar yadda NAIJ.com ta samu rahoto daga majiya mai karfi, za’a fitar da kayataccen shirin ‘Hakkunde’ a ranar 25 ga watan Yulio 2017.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga wani bidiyon yar wasan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel