Hukumar soji sunyi arangama da yan ta’adda, sun samo makamai

Hukumar soji sunyi arangama da yan ta’adda, sun samo makamai

A ci gaba da yaki da ta’addanci, rundunar operation Lafiya Dole sun gudanar da sintirin yaki a yankin da ake zargin yan ta’addan Boko Haram na amfani da shi gurin hutawa.

Wasu daga cikin yan ta’ddan dake kokarin kai harin bazata ga hukumar sojin sun shiga musayar wuta.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya gayyato likitocinsa Najeriya, ya fasa komawa Asibitin Landan

Hukumar soji sunyi arangama da yan ta’adda, sun samo makamai

Hukumar sojin ta samo wani babur daga hannun yan ta'addan

A cewar wata sanarwa daga Birgediya Janar Sani Kukasheka Usmna, yace an gudanar da aikin ne a ranar Laraba, 29 ga watan Maris.

An samo wasu makamai da harsasai daga yan ta’addan koda dai wani soja ya ji rauni sannan kuma yana samun kulawar likita a yanzu.

Karanta jawabin a kasa:

Hukumar soji sunyi arangama da yan ta’adda, sun samo makamai

Makaman da rundunar soji ta kwato daga yan ta'addan

A yau, Laraba 29 ga watan Maris 2017, rundunar sojin bataliya 112, na hukumar sojin Najeriya dake Operation LAFIYA DOLE, sun gudanar da sintirin yaki a hanyar Boskoro, karamar hukumar Dikwa dake jihar Borno, inda ya kasance makwancin yan ta’addan Boko Haram.

A yayinda suke gabatar da aiki, rundunar sun hadu da wasu yan ta’addan Boko Haram wanda ake zargin sun fake a yankin ne don su kai ma rundunar harin bazata a hanyar Ajiri-Dikwa.

KU KARANTA KUMA: ‘Dalilin daya sa Buhari ke son Magu ya cigaba da rike EFCC’ – Hon Nwuke

Tawagar suntirin sun yi arangama da yan ta’addan sannan sun farma mutun daya daga cikin su sannan sun samo wani bindigar AK-47, Mujalla 1, harsasai 47.

Abun takaici soja daya ya samu rauni a lokacin aikin, an kuma dauki jarumin sojan zuwa asibitin sojoji inda yake samun kulawar likita.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kwanan nan NAIJ.com ta sadu da mutun mafi karfi a Najeriya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel