An bankado wata badakala a Hukumar lafiya

An bankado wata badakala a Hukumar lafiya

Hukumar NHIS mai ba da inshora a kan harkar lafiya ta gano wata badakala da ake tafkawa a Hukumar Inji shugaban na ta Farfesa Usman Yusuf

An bankado wata badakala a Hukumar lafiya

Shugaban Hukumar NHIS Farfesa Usman Yusuf

Farfesa Usman Yusuf shugaban Hukumar NHIS na kasa ya bayyana cewa sun gano wata badakala a hukumar bayan wani bincike da suka yi. Shugaban na Hukumar da ke bada inshora a game da harkar lafiya ya bayyana haka jiya kamar yadda NAIJ.com ta samu labari.

Farfesan yace bayan an yi bincike an gano akwai sunayen jama’a na bogi da ke cikin tsarin na NHIS har sama da 23, 000. Farfesan yace an yi amfani da na’ura ne wajen bankado wannan badakalar da za ta taimaki kasar adana makudan kudi har kusan Naira Miliyan 300 kowane wata. Farfesa Yusuf yace don haka ne ma wasu ke kokarin ganin bayan sa.

KU KARANTA: Buhari ya fasa komawa Ingila

Umar Yusuf ya bayyana wannan ne a lokacim da ya ke bada takardun shaida ga mataimakin jakadar kasar Birtaniya a Najeriya Harriet Thompson. An dai yi wannan taro ne a Birnin Tarayyar kasar Abuja.

A wani nazari da aka yi kuma an gano cewa kusan mutane miliyan 4 ke fama cikin rashin ruwa a yankin da Boko Haram su ka yi ta’adi. Boko Haram dai sun barnata kashi 75% na hanyoyin ruwa a Yankin na Arewa maso gabas.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An maka Andrew Yakubu a kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel