Mun ba ku nan da makonin 2 ku amince da Magu sannan ku dawo da Ndume ko kuma... – Inji Alhaji Nura Abubakar

Mun ba ku nan da makonin 2 ku amince da Magu sannan ku dawo da Ndume ko kuma... – Inji Alhaji Nura Abubakar

Alhaji Nura Abubakar Waziri ya yi alwashin mamaye majalisa nan da mako biyu idan ‘yan majalisar dattawan sun ki amince da Ibrahim Magu da kuma dawo da sanata Ali Ndume.

Alhaji Nura Abubakar Waziri ya ce a wata sako zuwa ga ‘yan majalisa: “Mun ba ku makonni biyu ku amince da Magu sannan ku dawo da sanata Ndume ko kuma mu tada muku kura.”

NAIJ.COM ta samu rahoto cewa Alhaji Nura Abubakar Waziri ya mika wannan sako zuwa ga 'yan majalisar dattawan Najeriya musamman shugaban majalisa Bukola Saraki cewa, idan dai don talakawa suke zama a majalisa, to su dawo da sanata Ali Ndume kuma su rantsar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa,EFCC.

Ya ce: “Saboda mun ga alama kuna baiwa shugaban kasa ciwon kai, musamman kai Saraki. Kuma wata majiya ta rawaito cewa ka ce za ka durkusar da kasar nan. Idan ba ka durkusar da ita ba, to mu talakawa zamu durkusar da kai.”

KU KARANTA KUMA: An saki tsohon gwamnan jihar Adamawa daga gidan yari

“Mun ba ku nan da makonni biyu idan ba ku canja kudurinku ba, to za mu kira zanga-zanga sama da mutum milyan 5 don mu mamaye majalisar.”

Wannan ne sakon Alhaji Nura Abubakar Waziri ga ‘yan majalisar dattawan Najeriya musamman sanata Bukola Saraki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon rikicin kabilanci tsakani Hausawa da Yarabawa a Ile-Ife

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel