Buhari ya gayyato likitocinsa Najeriya, ya fasa komawa Asibitin Landan

Buhari ya gayyato likitocinsa Najeriya, ya fasa komawa Asibitin Landan

A ranar Laraba 29 ga watan Maris ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canza shawara dangane da duba lafiyarsa, inda fasa komawa kasar Ingila domin ganawa da likitocinsa.

Buhari ya gayyato likitocinsa Najeriya, ya fasa komawa Asibitin Landan

Shugaba Buhari

Tun a ranar da shugaba Buhari ya dawo ne ya shaida ma yan Najeriya zai sake komawa kasar Ingilan don a cigaba da duba lafiyarsa, amma a yanzu shugaban ya canza shawara, inda ya gayyato likitocin nasa, kuma ana sa ran zasu hallara Najeriya a ranar Juma’a 31 ga watan Maris.

KU KARANTA:‘Ban ga dalilin taƙaddama tsakanin Sanatoci da Hamid Ali ba’ – Inji Dogara

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana ma Sahara Reporters cewar tun a ranar Laraba ne tawagar shugaban kasa suka fara tafiya kasar Ingila, inda suka bi jirgin Ethiopia, amma a yanzu haka an kira su daga fadar shugaban kasa cewa su dawo gida.

Majiyar ta shaida ma Sahara wasu jiga jigan jami’an fadar shugaban kasa ne suka bashi shawarar kada ya koma, bayan kwashe sati 7 a kasar waje, idan ba haka ba za’a cigaba da watsa jita jita da dama wanda ka iya shigar da kasar cikin rudani.

Cikin wani gajeren bayani da Buhari yayi a ranar daya dawo, shugaba Buhari ya shaida ma yan Najeriya cewa zai koma kasar Ingila don a cigaba da duba lafiyarsa nan bada dadewa ba. Sai dai sakamakon halin da siyasar kasar ta fada, shugaba Buhari ya fasa komawa.

Idan mai karatu bai manta ba NAIJ.com ta dauko rahotom tafiye tafiyen da shugaba Buhari yayi zuwa kasar Ingila a baya domin duba lafiyarsa. don a watan Yulin shekarar 216 sai da shugaba Buhari yaje birnin Landan don a duba lafiyar kunnensa.

Wannan lamari ya biyo bayan korafe korafe da wasu kungiyoyin kare dimukradiyya suke yi inda suke bukatar shugaba Buhari ya bayyana nawa ya kashe wajen duba lafiyar tasa yayin da yake kasar Ingila.

Cikin wadanda suke bukatar sanin kudin da aka kashe wajen duba lafiyar shugaban akwai lauya Femi Falana, da sauran kungiyoyi kamar su SERAP, inda suka ce tunda dai Buhari na takama da shi mai gaskiya ne, toh sai ya fada ma yan Najeriya nawa ya kashe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon ranar da shugaban kasa Buhari ya dawo daga duba lafiyarsa a kasar Ingila

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel