‘Dalilin daya sa Buhari ke son Magu ya cigaba da rike EFCC’ – Hon Nwuke

‘Dalilin daya sa Buhari ke son Magu ya cigaba da rike EFCC’ – Hon Nwuke

Wani kwararre Onorable Ogbonna Nwuke ya bayyana dalilin da yasa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage kan lallai sai Magu a matsayin shugaban EFCC, Nwuke yace daga gani akwai wani abu na musamman da Buhari ke so dangane da Magu.

‘Dalilin daya sa Buhari ke son Magu ya cigaba da rike EFCC’ – Hon Nwuke

Shugaba Buhari

A baya dai majalisar dattawa ta ki amincewa da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC, sa’annan a kwanan nan sai tayi watsi da tantance kwamishinonin hukumar zabe sakamakon cigaba da zaman Magu akan kujerar EFCC.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, Nwuke yace bai yi mamaki ba, saboda a yanzu haka shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki na fuskantar tuhuma daga EFCC kan zarginsa da suke yin a satar makuden kudaden kudi.

KU KARANTA: ‘Ban ga dalilin taƙaddama tsakanin Sanatoci da Hamid Ali ba’ – Inji Dogara

“Bai kamata ace ana samun rikici tsakanin bangaren shugaban kasa da bangaren majalisa ba, ta yadda bai dace ba ace a daidai lokacin da ya kamata shuwagabnnin kasar nan su hada hannu wajen yaki da cin hanci da rashawa sai ya kasance shugaban majalisar kansa ana tuhumarsa da rashawa.

“Lallai ta tabbatar akwai wani dalili mai karfi da yasa shugaban kasa Buhari ya dage akan lallai sai Magu, kuma a ganina wadannan dalilan ne suka kawo rikici tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da bangaren majalisar dattawa. Amma tunda kaga Buhari ya dage, toh wata kila ya samu wasu bayanai ne wanda shi Bukola bai sani ba. Don haka nake bada shawara Buhari ya tattauna da Saraki.

“Ina ganin idan suka tattauna, zasu samar da mafita a tsakaninsu don shawo kan rikicin daya addabi bangarorin biyu. Ina ganin ya kamata kowa da kowa ya bada gudunmuwa wajen ganin an cimma manufar da aka sa a gaba, don tabbatar da manufofin jam’iyyar APC.

“Na san akwai rabe raben ikon mulki a tsakaninsu, amma dai ya kamata Saraki yayi biyayya da shugaban kasa ganin cewa tare da shi aka yi masa yakin neman zabe.” Inji Nwuke

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon tsohon shugaban hukumar NNPC da aka gurfaar dashi gaban kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel