Sanatoci 4 da sukayi magana kan dakatad da Ndume

Sanatoci 4 da sukayi magana kan dakatad da Ndume

An dakatad da tsohon shugaban masu rinjayen majalisar dattawa a yau Larabam 29 ga watan Maris akan laifin cewa yayi tuhume-tuhume ga abokan aikinsa Bukola Saraki da Dino Melaye ba tare da hujja kwakkwara ba

Sanatoci 4 da suka taimaka wajen dakatad da Ndume

Sanatoci da Sanata Ndume

Jaridar NAIJ.com ta bada rahoton cewa an dakatad dashi na tsawon watanni 6

Jaridar NAIJ.com ta tattaro muku sanatocin da suka baya goyon bayan wajen dakatad da shi a yau.

1. Sanata Barau Jibrin

Barau yace duk wani abu da mutum ya gani akan wani sanata kama yayi a tattauna a cikin gida kafin a yada.

Yace " Idan muka ga wani abu akan wani Sanata, wajibi ne mu kawo majalisa kafin muyi wasu maganganu.”

KU KARANTA: An dakatad da Ali Ndume a majalisa

2. Sanata Yusuf Abubakar

Yace : “A matsayinsa na mai laifi, kamata yayi a dakatad da Ndume daga ayyukan kwamiti amma bawai daga majalisa ga baki daya ba”

3. Sanata Mathew Uroghide

Kwamitin da’a a majalisa ta bayar da shawara cewa a dakatad da Ndume na tsawon zaman majalisa 191. Amma Mathew Uroghide yace a taimaka a rage shi zuwa watanni 6.

4. Ike Ekweremadu

Game da cewarsa , wannan zai zama darasi ga kowani sanata. Yayi kiraga sanatoci cewa suyi bincike cikin al’amura sosai kafin maganganu.

Magana akan dakatad da Ndume, mataimakin shugaban kasa akan labari, Lauretta Onochie, tace sanatoci na abu Kaman yara.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel