Gwamnatin tarayya ta samar da gidan fursunan mata na biyu

Gwamnatin tarayya ta samar da gidan fursunan mata na biyu

A ranar Laraba, hukumar gidan yari na Najeriya (NPS) ta sanar da samar da gidan fursunan mata na biyu a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta samar da gidan fursunan mata na biyu

Gwamnatin tarayya ta samar da gidan fursunan mata

Peter Tenkwa, mai kula da hukumar NPS a Adamawa, ya tabbatar da hakan a wata hira tare da hukumar dillancin labaran Najeriya a Yola.

KU KARANTA KUMA: Rikicin majalisa da Ibrahim Magu: Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani

Mista Tenkwa ya bayyana cewa ci gaban ya biyo bayan sake fasalin hukumar fursunan Najeriya bisa ga jinsi.

“Hukumar gidan yari na Najeriya ta samar da gidan yarin mata na biyu a Najeriya bayan gidan yarin mata dake Kiri-kiri a Lagas.

“tsohon fursunan Numan dake Adamawa ya zama fursunan mata na biyu dake Najeriya a yanzu wanda zai dauki fursunaoni guda 400; a yanzu fursunoni shidda ne a gidan yarin,” cewar Mista Tenkwa.

Ya bayyana cewa yan ta’addan Boko Haram sun hallaka fursunoni bakwai cikin 17 dake jihar a lokacin da ya fara aiki a watan Yuni na 2016.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan jihar Zamfara yayi sama da faɗi da N500m cikin tallafin da Buhari ya baiwa jihohi

A cewar sa, tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar da sashin hukumar gidan yarin Mubi, an gyara gidan yarin Maiha da Ganye sannan kuma aka dawo da aiki a cikin su.

Mista Tenkwa ya bayyana cewa a yanzu haka, gidan yarin Mubi, Maiha da Ganye na da fursunoni 184, 43 da 145 a kowanne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

A bidiyon kasa NAIJ.com ta tambayi yan Najeriya idan sunyi dana sanin zaben da sukayi a baya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel