Malamin sakandari ya ɗibga ma dalibarsa ciki a garin Minna

Malamin sakandari ya ɗibga ma dalibarsa ciki a garin Minna

Mataimakin shugaban makarantar sakandari dake garin Tunga-Minna, Malam Mohammed Kuyizhi ya gurfana gaban hukumar kare hakkin yara kan zarginsa da yi ma dalibarsa ciki da aka yi.

Malamin sakandari ya ɗibga ma dalibarsa ciki a jihar Minna

Dalibai mata

Shi dai Malam Kuyizhi ana zarginsa ne da yi ma dalibarsa mai shekaru 16 ciki.

Babban daraktan hukumar Hajiya Mariam Kolo ce ta jagoranci zaman a ranar Laraba 29 ga watan Maris inda ta bayyana cewa wani malamin makarantar ne ya kawo musu karar Malam Kuyizhi bayan mahaifin dalibar ya kawo karar wanda ake zargi gare shi.

KU KARANTA: An kai ma ɗaliban Najeriya hari a ƙasar India, an raunata 5 (Hotuna)

Kolo tace bayan sun samu rahoton ne sai suka aika ma wanda ake zargin daya bayyana gabansu don ya kare kansa, sai dai Kolo tace zasu mika lamarin zuwa ga hukumar yansanda don cigaba da gudanar da bincike.

“Mun riga mun mika dalibar asibiti don a tabbatar da lafiyarta, zamu tabbatar da an kwato mata hakkinta.” Inji Mariam Kolo. Ita ma dalibar ta bayyana ma hukumar cewa wanda ake zargin abokin mahaifinta ne na kud da kud, har ma yana yawan zuwa gidansu a kullum.

“Yarinyar ta fada mana wanda ake zargin yayi amfani da ita sau uku a ofishinsa, inda yake bata N50 ko N100 don yin kudin mota zuwa gida a duk lokacin daya sadu da ita.” Inji Kolo.

Bugu da kari dalibar tace mutumin ya bata wasu kwayoyi ta sha don ta zubar da cikin bayan ta sanar da shi dangane da ciki da take dauke da shi, amma ta ki yarda, kuma ta zubar da kwayoyin, amma daga bisani ta sha bayan malamin ya kara bata kwayoyin.

A cewar Kolo, dalibar tayi fama da matsanancin zafi bayan ta sha kwayoyin, hakan ya sanya dole ta fada ma iyayenta.

NAIJ.com ta samu rahoton cewa Malamin ya amsa laifinsa, amma sai yace yarinyar ce ta janyo sa har yayi mata ciki, sa’annan ya musanta cewa shi yayi mata ciki, amma daga karshe ya nemi afuwa, kuma yayi alkawarin daukan nauyin cikin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon wata dalibar Najeriya da aka karrama kasar Ingila

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel