Ministan tsaron Benin ya yi murabus

Ministan tsaron Benin ya yi murabus

- Ministan Tsaron Jamhuriyar Benin Candide Armand-Marie Azannai ya sauka daga mukaminsa saboda sabanin da suka samu da shugaba Patrice Talon na shirin sauya kundin tsarin mulki.

- Azannai ya sanar da murabus dinsa a shafin Facebook inda ya bayyana dalilai na halin da Benin ta shiga na sauyin siyasa.

Ministan tsaron Benin

Ministan tsaron Benin

NAIJ.com ta samu labarin cewa Shugaban kasar Patrice Talon ya bayyana shirin sauya kundin tsarin mulkin Benin musamman kan bukatar takaita wa’adin mulkin shugaban kasa zuwa wa’adi guda, matakin da wasu ‘yan siyasar kasar ke adawa da shi.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Zamfara yayi sama da fadi da makudan kudade

Shirin shugaban kasar dai ya sha bambam da na shugabanin Afirka da ke sauya kundin tsarin mulki don ci gaba da zama a karagar bayan kamala wa’adin su.

Majalisar Benin dai yanzu za ta gudanar da muhawara tare da kada kuri’ar amincewa da sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kuma kalli bidiyon wanda yafi kowa karfi a Najeria

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel