‘Ban ga dalilin taƙaddama tsakanin Sanatoci da Hamid Ali ba’ – Inji Dogara

‘Ban ga dalilin taƙaddama tsakanin Sanatoci da Hamid Ali ba’ – Inji Dogara

Kaakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya bayyana a ranar Talata 28 ga watan Maris cewa takaddama tsakanin majalisar dattawa da shugaban hukumar kwastam Hamid Ali wani hanya ne na kawar da hankulan yan Najeriya daga muhimman batutuwa dake gaban majalisar.

‘Ban ga dalilin taƙaddama tsakanin Sanatoci da Hamid Ali ba’ – Inji Dogara

Shugaban hukumar kwastam, Hamid Ali

Dogara ya bayyana haka ne lokacin daya karbi bakoncin shuwagabannin kamfanin jaridu a ofishinsa dake Abuja, inda yace batun sanya inifam din hukumar kwastam ba shi ya kamata ya zamo abin dubawa ba.

“Abu mafi muhimmanci shine yadda yake gudanar da aikin nasa” inji Dogara.

KU KARANTA: Rikicin majalisa da Ibrahim Magu: Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani

A satin data gabata ne dai majalisar dattawa ta bukaci a shugaban hukumar kwastam Hamid Ali da yayi murabusa daga kujerar dayake kai, saboda a cewarsu Hamid Ali bai dace ya rike kowanne irin mukami ba.

‘Ban ga dalilin taƙaddama tsakanin Sanatoci da Hamid Ali ba’ – Inji Dogara

Kaakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara

Majalisar ta dauki matakin ne biyo bayan rashin gurfanar Hamid Ali gaban majalisar dattawa cikin kakin jami’an hukumar ta kwastam tare da amsa tambayoyi kan zarge zarge da suke dashi akan sa. Ko a baya ma sai da majalisar ta fatattaki Hamid Ali yayin daya bayyana gabanta ba tare da ya sanya Kakin ba.

Wannan takaddama tsakanin Hamid Ali da majalisar dattawa ya faro ne lokacin da hukumar kwastam ta fitar da wani tsari na amsan kudaden fiton motocin da aka shigo dasu daga hannun yan Najeriya, sai dai bayan majalisar tayi watsi da tsarin, sai hukumar ta kwastam ta jingine batun tabbatar da tsarin. Amma duk da haka majalisar ta bukaci Hamid Ali ya gurfana gabanta sanye da Kakin hukumar kwastam.

Shi kuwa shugaban hukumar ta kwastam Hamid Ali ya ki gurfana gaban majalisar, inda yace wani lauya ya kai maganan gaban kotu, don haka ministan shari’a na kasa Abubakar Malami ya umarce su da kowa ya dakata har sai kotu ta yanke hukunci.

Sai dai hakan bai yi ma majalisar dattawan dadi ba, kamar yadda NAIJ.com ta tattaro bayanai, inda majalisar tace zata bukaci kawarta majalisar wakilai dasu sanya baki wajen ganin Hamid Ali yayi murabusa daga bakin aikinsa.

Jin hakan ne ya sanya kaakakin majalisar ta wakilai Yakubu Dogara fadin cewa ba zai iya daukan mataki kan batun ba, inda yace sai dai idan yan majalisa sun zauna gabaki dayansu, ta hanyar ne kadai za’a iya daukan mataki.

“Bani da hurumin yanke hukunci akan wannan batu da yawun majalisa, majalisar ce kadai zata ita tabbatar da matakin daya kamata mu dauka idan un hadu gaba daya. ba zan iya tabbatar da yadda matakin zata kasance ba” inji Dogara.

Daga karshe Dogara ya bayyana cewa suna aiki kafada da kafada da majalisar dattaw a matsayinsu na majalisun dokokin kasa, amma ya shawarci yan Najeriya dasu karkatar da hankulansu kan menene doka tace game da sanya Kakin, ba wai matsayin Ali ko na majalisa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon wasu ma'aikata dake zanga zanga a jihar Legas

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel