Jerin sunayen ministocin da Buhari ya aika ma majalisa (Karanta)

Jerin sunayen ministocin da Buhari ya aika ma majalisa (Karanta)

Majalisar dattawa ta bayyana sunayen mutane biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika mata don tantancewa don ya nada su mukaman ministoci.

Jerin sunayen ministocin da Buhari ya aika ma majalisa (Karanta)

Shugaba Buhari

Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ne ya bayyana haka a zaman majalisar na ranar Laraba 29 ga watan Maris.

KU KARANTA: Rikicin majalisa da Ibrahim Magu: Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani

Sunayen sun hada da:

Farfesa Steven Ocheni daga jihar Kogi

Da kuma Suleiman Hassan daga jihar Gombe

Shi dai Farfesa Ocheni zai maye gurbin marigayin James Ocholi ne, tsohon minista dake wakiltan jihar Kogi daya rasu sakamakon hadari akan hanyar Kaduna zuwa Abuja a shekarar data gabata.

Sai Malam Hassan daya fito daga jihar Gombe, wanda zai maye gurbin Amina Mohammed data samu cigaba da koma aiki a majalisar dinkin duniya a matsayin mataimakiyar sakatare.

Bayyana sunayen ministocin a majalisar dattawan ya biyo baya fatali da majalisar tayi da tantance mutanen da shugaba Buhari ya aiko musu wadanda yake muradin nada su mukaman kwamishinoni a hukumar INEC.

NAIJ.com ta ruwaito cewa majalisar ta dakatar da tantancewar ne sakamakon cigaba da zaman dirshan da shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ke cigaba dayi, wanda tace hakan bai dace ba, tun da dai ta riga ta tabbatar ba zai iya rike mukamin ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon da yan Najeriya ke bayyana ra'ayinsu dangane da mulkin Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel