Za mu kama duk wanda mu ka samu da rashin gaskiya-Hamid Ali

Za mu kama duk wanda mu ka samu da rashin gaskiya-Hamid Ali

Shugaban Hukumar Kwastam na kasa ya bayyana cewa karshen duk wani mugun iri da bata-gari a Hukumar ya zo don kuwa ba zai sassauta ba

Za mu kama duk wanda mu ka samu da rashin gaskiya-Hamid Ali

Kanal Hamid Ali na gidan kwastam yace karshen mugun iri ya zo

Kanal Hamid Ali mai ritaya ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifi a gidan kwastam din ba zai ji da dadi ba. Hamid Ali yace za a hukunta duk wani Ma’aikaci da aka samu da rashin gaskiya kamar yadda doka ta tanada.

Hamid Ali yake cewa zai yi kokari wajen hana fasa kauri sannan kuma ya nemawa kasar kudin shiga. Kanal Ali ya gargadi Ma’aikata da su guji yin ba daidai ba wajen duba kayan da aka shigo da su cikin kasar.

KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya hana Majalisa aikin ta

Za mu kama duk wanda mu ka samu da rashin gaskiya-Hamid Ali

Karshen bata-gari ya zo a gidan Kwastam

Kungiyar ANLCA sun koka da yadda ake samun cudani wani lokaci tsakanin Hukumar kwastam da sauran Hukumomi kamar ‘yan sanda wanda su ka ce hakan na ba su matsala wajen shigo da kayan da su ka sayo zuwa cikin kasar.

Kwanaki Hamid Ali ya bayyana cewa aikin na sa ba abu ne mai sauki ba tun farkon hawan sa har zuwa yanzu. Hamid Ali yace ya iske wasu manya ‘yan kasuwa da ke shigo da kaya daga kasar waje da suka yi kane-kane kan dokokin kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shekaru 2 kenan da zaben shugaba Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel