Boko Haram: Bam yayi barna a Jihar Borno

Boko Haram: Bam yayi barna a Jihar Borno

Jami’an tsaro sun bakunci lahira sannan kuma wasu su ka jikkata a lokacin da wani bam ya tashi a Garin Dikwa da ke Jihar Borno

Boko Haram: Bam yayi barna a Jihar Borno

Wani bam yayi barna a Borno

A daidai kan hanyar Maiduguri a Garin Dikwa ne wani bam ya tashi inda Jami’an tsaro har 2 su ka ce ga Garin ku nan. Haka kuma wasu mutane kusan 3 su ka jikkata a yayin da aka taka wani bam da ‘Yan Boko Haram su ka dasa.

Wannan mummunan abu ya faru jiya ne a Jihar Borno kamar NAIJ.com ke samun labari. Irin bam din nan na taba-ya-tashi ne yayi sanadiyar mutuwar ‘yan kato da gora a Garin Dikwa yayin da su ka shiga farautar ‘Yan Boko Haram.

KU KARANTA: Boko Haram sun kai hari a wasu Kauyuka

Boko Haram: Bam yayi barna a Jihar Borno

Boko Haram: 'Yan kato da gora sun rasu a wani hadarin bam

Wani Dan kato da gorar yace wannan abu ya faru ne bayan sun yi nasara kan wasu ‘Yan Boko Haram. A hanyar dawowa ne dai motar su ta fada kan wani bam nan take motar ta tarwatse inda wannan mummunan abu ya faru. Yanzu dai ana can ana jinyar wadanda su ka raunata.

Jiya ne kuma shugaban Jami’ar NOUN Farfesa Abdallah Uba Adamu ya bayyana cewa Fursunoni ma suna iya karatu a Jami’ar daga gidan yari yanzu ma dai har wani Dan kaso ya dawo zai yi Digiri na uku.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wadanda rikicin Boko Haram ya afka da su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel