Abin kunya takardar shaida: Sanata Dino Melaye zai kai ƙara mai SaharaReporters kotun New York

Abin kunya takardar shaida: Sanata Dino Melaye zai kai ƙara mai SaharaReporters kotun New York

- Sanata Melaye ya sanar da cewa zai ke ƙarar Omoyele Sowore zuwa ga wani kotu a New York ranar Jumma'a 31 ga watan Maris

- Ya ce zai kai ƙaran Sowore domin yana takura mishi

- Aranar Litinin 27 ga watan Maris, Shugaban Majalisar Dattijai akan maganan, Samuel Anyanwu, ya sa Dino Melaye a kan rantsuwa

Sanata Dino Melaye zai ja Sahara Reporters har wani kotu a Amurka

Sanata Dino Melaye zai ja Sahara Reporters har wani kotu a Amurka

Sanata Dino Melaye ya kammala tsare-tsaren domin ya kai karan mai SaharaReporters, a wani kotun New York. Ya ce zai kai ƙaran Sowore domin yana takura mishi a filin ‘Cyber’. Melaye ya fada cewa zai bada kofin magagari na ƙara a ofishin jakadancin Amurka sa’o’i bayan Mataimakin Shugaban jami’a Ahmadu Bello (ABU) ya tabbatar da cewa Sanata Dino Melaye ya sauke karatu daga jami'ar. A nashi gani, wannan tabbatarwa ya barrantar shi na abin kunya takardar shaidar.

KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya taka mana burki Inji Bukola Saraki

Sanata Melaye ya sanar da cewa zai ke ƙarar Omoyele Sowore akan ‘Cyberstalling’ zuwa ga wani kotu a New York ranar Jumma'a 31 ga watan Maris.

NAIJ.com ya ruwaito cewa Sanata Dino Melaye ya sa rigar ilimi sa wajen zaman Majalisar Dattawa omin ya nuna cewa ya sauke karatu daga jami’a da aji uku a cikin karatun yanayin kasa.

Melaye wanda farkon digiri sa ya zo karkashin bincike a cikin 'yan makonni,' yan sa'o'i, bayan ya bayyana a cikin jam'iyya majalisar dattijai a ranar Talata 28 ga watan Maris, ya saka a kan Twitter shirinsa na ziyarci Amurka domin ya ke ƙara. Duk da haka nan, Dan majalisar ya nace cewar, ya sauke karatu daga dayan jami'o'i da sun fi tsufa a Najeriya..

KU KARANTA: Yadda Ibrahim Magu ya addabi Sanatoci bayan an ki tabbatar da shi

A halin yanzu, a lokacin da ana jin maganar a ranar Litinin 27 ga watan Maris, Shugaban Majalisar Dattijai akan maganan, Samuel Anyanwu, ya sa Dino Melaye a kan rantsuwa, ya sa shi ya bayyana domin akwai wani kuka da wani abokin aiki, Sanata Ali Ndume ya yi da cewa shi Melaye na yawo da takardar shaidar daga Jami'ar Ahmadu Bello na , Zaria da ba daidai ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

A wannan bidiyo, za ka ga damuwar abin kunya takardar shaidar ta Melaye ta zurfafa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel