Gwamnan jihar Zamfara yayi sama da faɗi da N500m cikin tallafin da Buhari ya baiwa jihohi

Gwamnan jihar Zamfara yayi sama da faɗi da N500m cikin tallafin da Buhari ya baiwa jihohi

Majiya mai karfi ta bayyana ma jaridar Sahara Reporters yadda gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya karkatar da Naira miliyan 500 daga tallafin kudin bashin Paris da gwamnatin tarayya ta baiwa jihohin kasar nan 36.

Gwamnan jihar Zamfara yayi sama da faɗi da N500m cikin tallafin da Buhari ya baiwa jihohi

Gwamnan jihar Zamfara, Abdul Aziz Yari

Rahoton Sahara Reporters ya bayyana majiyar daga hukumar yaki da zamba da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bayyana mata cewar gwamnan jihar Zamfara Abdul Aziz Yari ya cire naira miliyan 500 daga naira biliyan 19 da jihar Zamfara ta samu zuwa asusun kungiyar gwamnonin Najeriya, inda daga nan sai ya mayar da kudin zuwa asusun biyan bashin siyan gida.

KU KARANTA: ‘Laifi tudu ne, take naka ka hango na wani’ – Shehu Sani ga Gwamnonin Najeriya

Bugu da kari EFCC ta bayyana ma jaridar The Nation cewa “Cikin naira biliyan 19, mun gano gwamnan ya gayyaci wata kamfanin kwararru, inda ya basu naira biliyan 2.2, daga nan su kuma suka mayar mai da naira miliyan 50 daga cikin biliyan 2.2.”

Bayan gwamna Yari ya amshi naira miliyan 500 din ne sai ya biya wata bankin wani kaso cikin bashin da take binsa na naira miliyan 800 wanda ya ranta ya siya gida a shekarar 2013. Sai dai majiyar ta bayyana cewar gwamnan yayi ciniki da bankin, inda suka yarda suka rage masa bashin daga N800m zuwa N500m.

Sai dai NAIJ.com ta ruwaito hukumar EFCC ta bi kadin kudaden sakamakon tana da masaniya kudin na jihar Zamfara ne daga cikin kudin bashin Paris da gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi, kuma ake kokarin karkatar dasu, ganin haka sai bankin ta mika ma EFCC naira miliyan 500 din sukutum.

Rahoton karkatar da kudin da gwamnan jihar Zamfara yayi ya bayyana ne kwanaki kadan bayan jaridar Sahara Reporters ta ruwaito binciken da EFCC take yi ma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki dangane da rawar daya taka wajen yin waka-ci waka-tashi da naira biliyan 3.5 na kudin Paris da suka sanya a wani asusun ajiyar kudi na bankin Access.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon tsohon shugaban NNPC da hukumar EFCC ta gurfanar a gaban kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel