Ba za’a yi wa Nnamdi Kanu shari’a a kotun Shari'ar Musulunci ba - IPOB

Ba za’a yi wa Nnamdi Kanu shari’a a kotun Shari'ar Musulunci ba - IPOB

- Ko da wani ɓangare na Arewacin Najeriya da akwai Yawanci Musulmi, babu wanda aka yi wa shari’a a asirce

- Kar a yi kuskuren yin shari’ar Nnamdi Kanu ta hanyar Shari’ar Musulunci

- shirun da Majalisar Dinkin Duniya da kuma duniya da baki daya, suka ci gaba da yi, zai iya zama abin hadari

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa an tsare Nnamdi Kanu tun 28 ga watan Disamba, shekara 2015

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa an tsare Nnamdi Kanu tun 28 ga watan Disamba, shekara 2015

IPOB sun ce akwai wani mãkirci na yin shari’a shugaban su ta hanyar Shari’ar Musulunci. Kungiyar Biyafara ta ce duniya ta yi shiru a zãlunci da ana yi wa mutane Igbo. Sun ce shirun da Majalisar Dinkin Duniya da kuma duniya da baki daya, suka ci gaba da yi, zai iya zama abin hadari.

'Yan asalin Mutane Biyafara (IPOB), sun ce da aka ci gaba da tsare shugabansu, Nnamdi Kanu, wani ƙeta ne, ba akan hakkin Kanu kawai ba, amma kuma akan doka.

KU KARANTA: Wata kunyiyar musulmai tayi taro a Abuja, ta yabawa Gwamnatin Buhari

Kar a yi kuskuren yin shari’ar Nnamdi Kanu ta hanyar Shari’ar Musulunci, IPOB sun yi wannan gargadi a ranar Litinin, 27 ga watan Maris 27. Sun ce da duk wani ƙoƙari na yin shari’a ko tsare shugaban, Mazi Kanu, a karkashin Shari'ar Musulunci, zai kawo matsala. NAIJ.COM sun ruwaito cewa, kungiyar Biyafara sun nace cewa idan aka yi mishi shari’a ta hanyar Musulunci, zai zama karin laifi ga ‘yan kungiyoyin Biyafara a Najeriya.

Mai kafofin watsa labarai da kuma tallace-tallace, da sakataren IPOB, Mista Emma Powerful, a cikin wata sanarwa a Awka, ya hada abin da kungiyoyin zanga-Biyafara suke fiskanta yanzu kamar misãlin abin da mutane Biyafara na lokacin 1967 -1970 suka fiskanta kafin aka fara yakin sanadiyar da aka rasa rayukan mutane (Kiristoci) da yawa.

KU KARANTA: An ɗaure matashi watanni 9 a gidan yari kan ya zagi gwamna Masari

Da yana kwatanta zargin yin shari’ar Kanu da sauran mutane da aka tsare ta hanyar Shari'ar Musulunci, Mista Powerful ya lura da cewa ko da wani ɓangare na Arewacin Najeriya da akwai Yawanci Musulmi, babu wanda aka yi wa shari’a a asirce a karkashin tsarin Shari'ar Musulunci tun daga halittar Najeriya ta Birtaniya a shekara ta 1914. Ya kuma yi mamaki me zai sa Nnamdi Kanu da kuma sauran Kiristoci a kudancin Najeriya su fiskanci irin wannan shari’a.

Kakakin IPOB ya ce ya nuna rashin adalcin Justice Binta Nyako na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ya juya daga harkokin shari'a a karkashin doka na kowa, zuwa ga Shari’a ta Musulunci.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa/ Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan bidiyo na nuna Nnamdi Kanu yana magana daga kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel