Ba kan ta: Majalisa za tayi wa shugaba Buhari bore

Ba kan ta: Majalisa za tayi wa shugaba Buhari bore

A Yau ne wasu ‘Yan Majalisa suka nuna cewa za ayi ta ta kare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a dalilin kin sallamar Ibrahim Magu daga EFCC

Ba kan ta: Majalisa za tayi wa shugaba Buhari bore

Shugaba Buhari ya ki sallamar Magu daga aiki

Wasu ‘Yan Majalisa sun nuna bacin ran su a yau dinnan inda suka kulla damarar kin amincewa da duk wani sabon mukami da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada kuma zai biyo ta hannun su a dalilin takadammar da ake bugawa da Ibrahim Magu na EFCC.

Majalisar ta yi watsi da jerin sunayen da shugaba Buhari ya turo na sababbin Kwamishinonin Hukumar zabe na INEC. ‘Yan Majalisar dai suna jin haushi ne bayan shugaban kasar ya ki sallamar Ibrahim Magu daga aikin Hukumar EFCC bayan Majalisar ta ki amincewa da shi har sau biyu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yabawa Bola Tinubu

Ba kan ta: Majalisa za tayi wa shugaba Buhari bore

Yaki zai barke tsakanin shugaban kasa da Sanatoci

Shugaban Majalisar Bukola Saraki da wasu ‘yan Majalisar sun nemi ‘Yan Majalisun su guji watsi da jerin sunayen da shugaban kasa ya aiko. Don haka ne ma suka yarda su sake kallon sakon shugaban kasar amma bayan mako biyu.

Yanzu haka kuma bayanan da suke zuwa mana nan NAIJ.com sun sun nuna cewa Sanata Ali Ndume mai wakiltar kudancin Borno a Majalisar Dattawa ya jefa kan sa cikin babbar matsala bayan da ya nemi Majalisa ta binciki shugaban ta Bukola Saraki da kuma Dino Melaye.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bayan shugaba Buhari ya dawo daga Ingila

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel