"Musabbabin rikicina da Dangote" – Gwamna

"Musabbabin rikicina da Dangote" – Gwamna

Gwamnan jihar Ogun Sanata Ibikunle Amosun ya danganta musabbabin rikicinsa da Dangote da yadda hamshakin attajirin ke nuna halin ko in kula da kyautata ma al’aummar yankin da kamfaninsa ke zaune.

"Musabbabin rikicina da Dangote" – Gwamna

Gwamna Amosun

Gwamnan ya bayyana wannan dalilin a matsayin abinda ya kawo tabarbarewa dangantaka tsakaninsa da Aliko Dangote da kuma kamfanin Dangoten kansa. Gwamnan ya bayyana haka ne yayi gudanar da taron manema labaru a ofishinsa dake Abekuta.

KU KARANTA: Shugaban DSS, Abba Kyari da Mamman Daura sun shirya maƙarƙashiya don a tsige Magu daga EFCC

Gwamnan ya bayyana cewar manyan motocin kamfanin Dangote dake dakon kayayyakin kamfanin na daga cikin abubuwan dake lalata hanyoyin jihar sakamakon nauyinsu, abin haushin ma kamar yadda NAIJ.com ta gano shine kamfanin Dangote basa tabuka komai wajen ganin sun gyara hanyoyin.

“Dalilin daya sa nake rigima da Dangote shine manyan motocin kamfaninsa suna bata mana hanya, misali shine titin Ilaro-Papalanto, ba kananan motocin mutanenmu bane ke bata hanyar, manyan motocin kamfanin Dangote ne.” inji Gwamna Amosun.

Gwamnan yace a maimakon kamfanin ta taimaka wajen gyaran hanyar, amma sai tayi shiru, duk da cewa mun san suna samun makudan kudade a jihar.

Daga karshe gwamnan yace ya kamata kamfanin Dangote su zage kaimi wajen gudanar da ayyukan kyautata ma al’ummar jihar, inda yace gwamnatin jihar ta kammala shirin biyan yan kwangila kudadensu don su dawo bakin aiki su kammala gine ginen hanyoyin da aka fara a jihar tun a bara.

Amosun yace sun biya yan kwangilar ne da kudaden bashin Paris Club da aka biya su, yace:

“Zamu tabbatar da kammala duk wani aikin da muka fara kafin mu bar mulki, muna fata gwamnati zata sake biyan mu sauran kudaden Paris. Muna so gwamnatin tarayya ta bamu dukkanin titunan ta dake jihar don mu gyara su.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon Gwamna Amosun yana tuka matarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel