Wata sabuwa! An bankado Saraki cikin wata almundahana ta naira biliyan 3.5

Wata sabuwa! An bankado Saraki cikin wata almundahana ta naira biliyan 3.5

NAIJ.com ta samu labarin cewa Shugaban Majalisar dattawan Nijeriya, Bukola Saraki ya musanta duk wani hannu a badaƙalar wawure naira biliyan 3.5 a cikin wasu kuɗaɗe na bashi da ƙasashen Paris Club suka yafe wa ƙasar.

Saraki tare da Dino

Saraki tare da Dino

Kafofin yaɗa labarai a Nijeriya dai sun bayar da rahotannin yadda wani rahoton hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasar ta'annati EFCC ya shaida wa shugaba Muhammadu Buhari, cewar Sanata Saraki ya yi amfani da mataimakin shugaban ma'aikatansa da kuma wasu jami'ansa wajen halarta kuɗin haram.

Rahoton ya bayyana yadda Mista Saraki ya hada mataimakin shugaban ma'aikatansa da waɗanda suka tuttura kuɗaɗen zuwa asusun bankunan da ke da alaƙa da shi.

Rahoton na EFCC ya ce za a iya tuhumar shugaban majalisar da waɗanda suka taimaka masa da laifin halarta kuɗin haram.

KU KARANTA: Jami'an DSS sun kama mataimakin Shekau

NAIJ.com ta samu labarin cewa Yusuph Olaniyonu, ya musanta rahoton, yana mai cewar wani matakin ramuwar gayya ce daga muƙaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, wanda majalisar dattawan Nijeriya ta ƙi tabbatar da shi a matsayin cikakken shugaba.

Rahotanni sun ce yayin da aka miƙa rahoton wannan badaƙala ga shugaba Buhari ranar 10 ga watan Maris, ita kuwa majalisar dattawan a ranar 15 ga watan ne ta ƙi tabbatar da Ibrahim Magu a mukaminsa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli yadda wani Gwamna ya tuka matar sa cikin mota a bainar jama'a

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel