Majalisar wakilai ta hau kujerar na-ki game da Ibrahim Magu

Majalisar wakilai ta hau kujerar na-ki game da Ibrahim Magu

Majalisar wakilan Najeriya, ta ce tana nan a kan matsayinta, na kin amincewa da Ibrahim Magu, ya zama shugaban hukumar masu bata dukiyar kasa ta Najeriya, (EFCC).

NAIJ.com dai ta samu labarin cewa shugaban kwamitin labarai na majalisar dattawan Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce batun Ibrahim Magu, babu shi, sai dai fadar shugaban kasar ta sake tura masu wani mutum na daban kamar yadda ya bayyana a hirarsu da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari.

Shugaban EFCC Ibrahim Magu

Shugaban EFCC Ibrahim Magu

NAIJ.com dai ta samu labarin cewa Da yake Magana akan shugaban hukumar Kwastam, Kanal Hamid Ali, mai ritaya, Sanata Sabi Abdullahi, ya ce majalisar dattawan ta yanke matsayinta na tilas yayi murabus.

KU KARANTA: An tsige mutane da dama a cikin Gwamnatin Buhari

Dan majalisar dattawan ya yi wannan bayani ne a lokacin bude wani taron bita da aka shirya ma wasu malaman Firamare, a garin Kontagora dake jihar Neja, da nufin kyautata harkokin koyarwa a yankin.

Malaman firamaren guda dari da ashirin 120, ne aka shiryawa wannan horaswa ta musamman da Sanata Sabi Abdullahi, ya ce ya kashe sama da kudi Naira Miliyan Goma sha Biyar domin basu horon.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

A wannan yanayi na matsi, ko N1000 zata iya yi maku cefane?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel