Kwastam ta kwace motoci 13 a gidan wani sanata a Kano

Kwastam ta kwace motoci 13 a gidan wani sanata a Kano

- Hukumar kwastam ta kwace motoci 13 a gidan wani sanata mai wakilci jihar Kano

- Hukumar ta ce har yanzu ba su tantance adadin farashin kudin motocin ba

Hukumar kwastam shiyar Kano ta killace gidan wani Sanata mai wakilci Jihar Kano da kuma kwace wasu motoci 13 da ake zargin boyewa a gidan sanatan.

kwamandan kwastam a shiyar, Bala Dole, ya bayyana haka a ranar Litinin, 27 ga watan Maris cewa motocin sun hada da sabon Toyota Hilux 12 da kuma Land Cruiser Jeep 1.

Dole bai ambaci sunan sanatan ba, ya ce an biyo motocin ne daga Maigatari a Jigawa bayan samu wani rahon sirri.

Kwamandan ya ce, sun kama motocin 210 tare da sauran abubuwa, ciki har da kayan abinci mai daraja miliyan 269.5 a jihohin Kano da Jigawa a cikin watanni takwas da ta gabata.

Ya ce sauran abubuwa da aka kwace a lokacin gudanar da binciken sun hada da; buhun shinkafa 9,757, supergetti na kasashen waje 2,916, kartanin man gyada na kasashen waje 2,770 da kuma kartanin macaroni 999.

“Har yanzu ba mu tantance adadin farashin kudin motoci 13 da aka kwace a gidan sanatan ba.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon tuhumar cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel