Ba za mu sake bari ‘Yan ta’adda su kwace wani yanki na kasar nan ba – Inji Buhari

Ba za mu sake bari ‘Yan ta’adda su kwace wani yanki na kasar nan ba – Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace Najeriya ba za ta sake yarda tayi sakaci wasu ‘yan ta’adda su kwace wani yanki na kasar nan ba.

Ba za mu sake bari ‘Yan ta’adda su kwace wani yanki na kasar nan ba – Inji Buhari

Shugaban kasa Buhari yace bazasu sake yin sakacin da wasu yan ta'adda zasu kwace wani yanki a kasar ba

Buhari ya fadi hakanne a dajin Sambisa wajen bude bikin wasannin soji na farko da za’ayi a dajin.

Ministan tsaro Mansur Dan-Ali ne ya wakilci shugaban kasan a wajen bude bikin wasannin sojin.

KU KARANTA KUMA: Hukumar Kastam ta kwace motocin wani sanata guda 13 a jihar Kano

Janar David Ahmadau wanda shine shugaban shirya wasan yace an shirya wannan gasar ne a dajin Sambisa saboda a nuna wa mutane cewa an fa kwato dajin daga hannun kungiyar Boko Haram sannan sojin Najeriya din ta mai da dajin filin gudanar da gasar ayyukan soji na kasa daga yanzu.

Yace za’a kara ne tsakanin sansanonin sojoji dabam da bam inda sansanin da tayi fice za a bata kofi, mai suna kofin babban hafsan sojin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Jami'an DSS sun kama mataimakin Shekau a wata kasuwa

A wani al'amari makamancin wannan, NAIJ.com ta ruwaito cewa yan gudun hijira 1,000 dake zaune a Ibadan, babban birnin jihar Oyo sun bayyana kudirinsu na son komawa yankunansu dake jihar Borno don fara sabon rayuwa bayan kakkabe yan ta’addan na Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kwanakin baya hukumar NAIJ.com ta dauko rahoton yadda mutanen Kudancin Kaduna ke rayuwa bayan rikicin da ya afku a yankin, kalli bidiyon a kasa:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel