Farashin Dala na kara sauka kasa

Farashin Dala na kara sauka kasa

Kamar dai yadda ku ka samu labari a jiya ne farashin dalar Amurka ya kara saukowa kasa zuwa N360 wannan dai ba karamin abin murna bane.

Farashin Dala na kara sauka kasa

'yan canji na kuka Dala na kara sauka kasa

Cikin wata guda kawo yanzu dai dala tayi wani mugun kifewa daga sama da N500 zuwa N360 a bankuna. A jiya ne bankin kasar watau CBN ya bada umarni bankuna su rika sayarda dala a kan N360 daga kusan N370 da yake.

KU KARANTA: An sace wasu 'yan kasuwa a Garin Sokoto

CBN ke cewa dole bankuna su dabbaga wannan doka domin a ko yaushe ana iya zuwa bincike. CBN din dai ya gargadi bankuna da su guji sayar da dalar da kowa face wanda yake neman kudi zai fita kasar waje karatu ko asibiti.

Farashin Dala na kara sauka kasa

Dala na kara sauka kasa

Yanzu dai dalar tayi araha da sauki a gari domin kuwa a cikin kwana guda ko biyu rak mutum zai samu kudin da yake so domin fita kasar waje. An dai haramtawa bankuna sayar da dala ga ‘yan canji.

CBN ta saki makudan miliyoyin dala wanda hakan ya sa ‘yan canji su ka sha kasa. A wancan makon kadai ‘yan canji sun rasa sama da Naira Miliyan 100. Dama dai NAIJ.com ta rahoto cewa ‘Yan kasuwa masu canjin kudi sun fara kokawa da lamarin tun tuni.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon farashin kayayyakin abinci

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel