Dino Melaye: Inda Jami'ar A.B.U ta bar baya da kura

Dino Melaye: Inda Jami'ar A.B.U ta bar baya da kura

Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ta wanke Sanata Dino Melaye ta ce ba shakka dalibin ta ne kuma ya kammala karatun sa sarai, amma sai dai.

Dino Melaye: Inda Jami'ar A.B.U ta bar baya da kura

Shugaban Jami'ar ABU Zaria

Sanata Dino Melaye mai wakiltar yammacin Kogi na fuskantar barazana game da shaidar karatun sa, sai dai yanzu Jami’ar ABU ta wanke sa inda bayan nan yayi ta tika rawa, amma fa da sauran aiki a gaban sa.

KU KARANTA: Da wuya idan har Dino Melaye ya kammala ABU

Dino Melaye: Inda Jami'ar A.B.U ta bar baya da kura

Sanata Dino Melaye lokacin zaman

1. Shugaban Jami’ar ABU ta Zaria Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana cewa Dino Melaye ya kammala karatun Digirin sa a Jami’ar inda ya fita da matakin 3rd class sai dai ma’aikatan da ke kula da harkokin jarrabawa a Jami’ar ba su yi na’am da wannan ba. Anya?

2. Ko ta ya Dino ya samu shiga Jami’a ba tare da ya ci jarabawar WAEC ta kammala Sakandare ba? Asali ma dai ya fadi takardar da yake so ya karanta watau Geography.

KU KARANTA: Sanata Melaye bai kammala karatu ba

3. Ya aka yi ake ta samun canjin suna a takardun Sanata Melaye? Wani lokaci ace Dino Melaye, can ka ji Melaye Daniel Jonah?

4. Me ya hana sa karbar satifiket din sa bayan kusan shekaru 20 da kammala makaranta?

5. Ta ya aka yi Dino Melaye yayi aikin bautar kasa a shekarar 1999 bayan shugaban Jami’ar ABU yace a shekarar 2000 Dino ya kammala karatun sa?

Dino Melaye: Inda Jami'ar A.B.U ta bar baya da kura

Acikin dakin majalisar dattawan Najeriya

Sai dai Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa ya canza sunan sa ne daga baya. Sanatan dai ya kawo takardu da za su goyi bayan sa inda ya rantse yayin da za ayi zaman.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Cigaban Najeriya da gyaran jirgin kasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel