"Bana hadahadar shigo da motoci, kuma bansa kowa ya shigo min da mota ba" - Saraki

"Bana hadahadar shigo da motoci, kuma bansa kowa ya shigo min da mota ba" - Saraki

Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya gurfana gaban kwamitin bincike na majalisar dattawa dake bincike kan zarginsa da ake yin a mallakan wata motar alfarma da hukumar kwastam ta kwace.

"Bana hadahadar shigo da motoci, kuma bansa kowa ya shigo min da mota ba" - Saraki

Sanata Saraki

A watan Janairu data gabata ne dai hukumar kwastam ta kama motar bayan ta gano takardunta na jabu ne, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Anyi zargin dalilin daya sanya majalisar matsa ma shugaban hukumar ta kwastam Hamid Ali, baya rasa nasaba da kwace wannan mota da jami’an hukumar suka yi.

KU KARANTA: Sulhu yaƙi tabbatuwa tsakanin Makarfi da Sheriff, an cigaba da kai ruwa rana

A ranar Litinin 27 ga watan Maris ne tsohon shugaban masu rinjaye Sanara Ali Ndume ya gabatar da koke gaban majalisar kan lallai ya kamata a bincike gaskiyar zargin da wata jarida tayi na cewa wai an kwace motar Bukola Saraki a tashar ruwa.

Sai dai Saraki ya bayyana ma kwamitin cewar bashi da masaniya dangane da shigo da motar, inda yace shi ba mai shigo da kaya bane, kuma bai sanya wani ya shigo masa da mota a madadinsa ba.

“Nagode ma mambobin kwamitin nan da suka gayyace ni, na farko dai ni ba mai shigo da kaya bane, kuma bani da wani wakili da na sanya ya shigo min da kaya.” Inji Saraki, kamar yadda NAIJ.com ta samu rahoto.

Shugaba majalisar dattawa ya bayyana cewa lallai sanatoci sai sun dage wajen kare martabar majalisar sakamakon akwai miyagun mutane masu son ganin sun bata ma majalisar suna, inda ya kara da cewa bambamcin mulkin soji dana farar hula shine majalisun dokoki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon wani mutum da yayi zargin Buhari ne shugaban masu cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel