Yankin Arewa zai samu wata katafariyar jami'ar kasa-da-kasa

Yankin Arewa zai samu wata katafariyar jami'ar kasa-da-kasa

- Jami'ar kasa da kasa ta kasashen Africa maso Gabas dake kamfala a kasar Uganda ta nemi izini domin kafa reshen jami'ar a jihar Kano

- Rokon hakan ya fito ne daga shugaban jami'ar Farfesa Dawoud Shenduda Dawoud wanda ke jawabi ga Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a lokacinda suka ziyarceshi a ofishinsa

Yankin Arewa zai samu wata katafariyar jami'ar kasa-da-kasa

Wata kofa a garin Kano

Farfesa Dawoud yace makasudin ziyarar tasu shine don inganta hadin gwiwa tsakanin jami'ar da Gwamnatin jihar Kano

Kawo yanzu dai akwai dalibai yan asalin jihar Kano kusan 400 dake karatu a jami'ar, wasu sun kammala karatu sun dawo wasu suna cigaba da karatunsu a cen a karkashin kulawar Gwamnatin Kano.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC bata iya mulki ba

Shugaban makarantar yace zasuyi hulda ne kai tsaye da Gwamnatin jihar ba tare da mai shiga tsakani ba ko jami'in tuntuba kamar yadda Gwamnatin baya tayi.

Gwamna Ganduje ya yi murna da ziyarar tasu a inda ya bukaci shuwagabannin jami'oin jihar Kano da sakataren hukumar tallafin karatu su tattauna da tawagar domin ganin yadda za kulla yarjejeniyar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel