Dalibar jami’ar Adamawa ta kashe kanta saboda bata ci jarabawa ba

Dalibar jami’ar Adamawa ta kashe kanta saboda bata ci jarabawa ba

A cewar wani rahoto da ya iso ma hukumar NAIJ.com, wata dalibar jami’ar kimmiya na Moddibo Adama wato Moddibo Adama University of Technology (MAUTECH) dake Yola ta kashe kanta bayan ta gano cewa ta fadi a darusa guda 9 da ta dauka.

Dalibar jami’ar Adamawa ta kashe kanta saboda bata ci jarabawa ba

Dalibar jami’ar Adamawa ta kashe kanta bayan ta sha maganin kwari

Dalibar ta jami’ar kimiyya dake Yola, jihar Adamawa ta kashe kanta ne ta hanyar shan maganin kwari a dakunan kwanan dalibai na Oba Adetona dake jami’ar sakamakon rashin kokari da batayi a jarabawar ta.

KU KARANTA KUMA: YANZU-YANZU: Yan ta'adda sun kai hari a wani gidan rawa

A cewar bayanai da aka tattara, wacce abun ya faru a kanta ta kasance daliba a sashin makarantar koyar kimiyyar labarai wato School of Management and Informatin Technology (SMIT).

An bayyana cewa ta kashe kanta ne bayan ta gano cewa ta fadin a jarabawar ta guda 9 na zagon farko a jami’ar.

NAIJ.com ta samu labarin cewa har yanzu hukumar makarantar bata yi wani jawabi a kan al’amarin ba.

A wani al'amari makamancin haka,wani dalibin makaranta ya kashe kansa ta hanyar rataya bayan budurwar sa ta kawo karshen soyayyar su.

KU KARANTA KUMA: Dalilai 4 da suka sa DSS ta dakatar da Magu

An bayyana cewa matashin da aka karya ma zuciya ya sami wani wasika daga budurwar sa wacce ta yanke shawarar kawo karshen soyayyar su. Wannan hukunci da ta yanke ya sa shi kashe kansa a take.

Kwanan nan NAIJ.com ta hadu da mutumin da yafi karfi a Najeriya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel