Yan gudun hijiran Borno 1,000 dake Ibadan sun shirya komawa gida

Yan gudun hijiran Borno 1,000 dake Ibadan sun shirya komawa gida

A yanzu haka sama da yan gudun hijira 1,000 dake zaune a Ibadan, babban birnin jihar Oyo sun bayyana kudirinsu na son komawa yankunansu dake jihar Borno don fara sabon rayuwa bayan kakkabe yan ta’addan na Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

Yan gudun hijiran Borno 1,000 dake Ibadan sun shirya komawa gida

Yan gudun hijira dake jihar Oyo na son komawa gida Borno

Sansanin yan gudun hijiran ya hada mutane daban-daban wadanda suka hada da matasa Musulmai da Kirista, mata da yara, sun gudanar da gangamin lumana a unguwar Ring Road dake Ibadan a karshen mako inda suka bayyana zuciyoyinsu kan kalubale daban-daban da suke fuskanta a matsayin yan gudun hijira tun shekaru uku da suka wuce.

KU KARANTA KUMA: “Da ni da El-Rufai muka rubuta ma Buhari wasikar nan” – Fasto Tunde Bakare

Da suke magana, shugabanninsu da sakatare, Mista Philemon Obadiah Aga da Mallam Amada Usman, sun fada ma manema labarai cewa koda dai jihar Oyo ta kasance gari mai tarin alkhairi da karrama baki, yawancin sun a fuskantar kalubale gurin samun aiki sannan kuma rayuwa tana yi masu wahala sosai.

“A halin yanzu, muna fuskantar kalubale na abinci da kiwon lafiya wanda ya hade da ciwon yunwa yayinda ‘ya’yanmu basa samun daman zuwa makarantu,” kakakin su yayi korafi.

Baya ga haka, a kullun suna gwagwarmaya da matsalar muhalli kamar yadda sama da mutane 10 ke zama a daki daya, yawanci a gine-ginen da ba’a kammala ba inda jami’an tsaro ke kama su.

Yayinda suke yaba ma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta kore yan ta’addan Boko Haram daga yankin Arewa maso gabas, musamman a yankin kudancin jihar Borno inda daga nan yawancin su suka fito, sun kuma roki gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Oyo da Borno da su taimaka gurin samar dabaru don komar dasu gida nan bada jimawa ba.

KU KARANTA KUMA: Dalilai 4 da suka sa DSS ta dakatar da Magu

Mun yanke shawarar komawa gida sannan mu fara sabuwar rayuwa ba tare da bata lokaci ba,” inji su.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel