Bafarawa yayi aman wuta, yace Buhari da APC basu iya mulki ba

Bafarawa yayi aman wuta, yace Buhari da APC basu iya mulki ba

Tsohon gwamna jihar Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa ya baiyana tsarin gudanarwa na mulkin kasa da jam'iyyar APC ke yi da zama wani tsari na kuskure ga saukaka matsalolin da al'umma suke ciki.

Bafarawa yayi aman wuta, yace Buhari da APC basu iya mulki ba

Bafarawa yayi aman wuta, yace Buhari da APC basu iya mulki ba

Bafarawa wanda ya nuna cewar hakika tsarin da APC take bi akwai kura-kurai masu hatsari ga ciyar da kasa gaba, yana nuna kasawar gwamnatin Buhari ga isar da manufofin da suka dace don tallafawa yan kasa.

KU KARANTA: Abun da rubuta ma Buhari gaskiya ne

"Mafi rinjaye wadanda suka yi tsayin daka don ganin samuwar jam'iyyar APC yanzu suna matsayin 'yan kallo, haka ma wasu ala dole sun bar ta saboda zalunci da cin amana da aka yi musu. Don haka jam'iyyar tana a tafarki na zama hanyar cin mutuncin juna da ha'inci abin da ya janyo talaka bai amfana da mulkin nata ba; saboda an koma ana fada ga neman mulki da ganin kyashin juna bisa son kai ba domin taimakawa al'umma ba." inji Bafarawa.

KU KARANTA: Hadda sa hannun fasto a cikin wasikar Elrufa'i zuwa ga Buhari

Dangane da haka ya nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya waiga baya ya gano irin wadannan kura-kurai ya kuma gyara idan har akwai son talaka da ci gaban kasa a zuciyarsa don ceto kasa daga mulkin da yanzu ake fuskantar wahaloli da kalubale masu yawa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli katafaren aikin da Buhari ya shimfida na samar da jirgin kasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel