Sulhu yaƙi tabbatuwa tsakanin Makarfi da Sheriff, an cigaba da kai ruwa rana

Sulhu yaƙi tabbatuwa tsakanin Makarfi da Sheriff, an cigaba da kai ruwa rana

An cigaba da cacar baki tsakanin bangaren shugabancin jam’iyyar PDP karkashin jagorancin halastacce shugabanta Sanata Ali Modu Sheriff da banagaren Sanata Ahmed Makarfi, duk da sulhun da suka yarjejeniya akai.

Sulhu yaƙi tabbatuwa tsakanin Makarfi da Sheriff, an cigaba da kai ruwa rana

Makarfi da Sheriff, an cigaba da kai ruwa rana

Musabbabin sake jan dagar kuwa bata wuce batun da Ali Modu Sheriff ya furta ba inda yace zai kai duk wani mahaluki daya kira Ahmed Makarfi da suna shugaban kwamitin riko, ko da ko yan jaridu ne, na biyu kuma shine sanar da daukar ma’aikatan da zasu yi hidima a babban ofishin jam’iyyar da Sheriff yayi.

Cikin wata sanarwa da mataimaikin Sheriff ya fitar, Dr Cairo Ojoughoh, yace Sheriff ya sanar da daukan ma’aikata aiki ne a don cike gurbin da tsofaffin ma’aikatan jam’iyyar suka bari, sakamakon yajin aiki da suka shiga.

KU KARANTA: Jami’an ýansanda na neman jikan Sir Ahmadu Bello Sardauna ruwa a jallo

Ganin haka sai Makarfi ya umarci ma’aikatan da suyi watsi da barazanar da Sheriff yayi musu, “Ba zamu dauki barazanar da Sheriff yayi ma ma’aikatan mu da wani muhimmanci ba, sakamakon shi mayaudari ne” inji sakataren watsa labaru na bangaren Makarfi, Dayo Adeyeye.

NAIJ.com ta ruwaito a makon data gabata ne bangarorin biyu suka rattafa hannu kan wata yarjejeniya da kwamitin sulhu karkashin gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ta samar, inda dukkaninsu suka yarda akan zasu yi aiki kafada da kafada da juna wajen sake gina jam’iyyar.

Sulhu yaƙi tabbatuwa tsakanin Makarfi da Sheriff, an cigaba da kai ruwa rana

Makarfi da Sheriff

Sheriff ya bayyana bangaren Makarfi a matsayin haramtacciyar kwamiti, sakamakon hukuncin da kotun daukaka kara dake jihar Fatakwal ta yanke a ranar 17 ga watan Feburairu. Sheriff yace: “Makarfi ya shiga taitayinsa, kada ya dinga shiga al’amuranmu, saboda bama sanya baki cikin harkokinsa.

“Idan ya kara fadin maganan data fi karfin bakinsa, toh zamu janye goyon bayan mu ga yarjejeniyar da muka cimmawa a baya, mun riga mun dauki sabbin ma’aikata da zasu cigaba da tafiyar da al’amuran jam’iyya, idan Makarfi ya ga dama ya cigaba da rike tsofaffin ma’aikatan.

“Mun gaji da irin wannan abu, don haka ya isa. Ba zmau bari wani karamin al’amari ya karkatar da hankulanmu daga manufar na mayar da jam’iyyar PDP ga hannun talakan Najeriya ba, don haka ba zamu kyale wani mai nufin kashe mana jam’iyya ya cigaba da yadda yake so ba.” inji Sheriff

Sheriff ya cigaba da gargadin tsofaffin ma’aikatan jam’iyyar dake rike da kayayyakin jam’iyyar PDP dasu tabbata sun dawo dasu ba tare da bata lokaci ba: “Duk wani dake rike da kayan jam’iyya ya tabbata ya dawo dasu cikin kwanaki 7, ko kuma mu mika su zuwa ga yansanda.”

Sai dai suma bangaren Makarfi ba suyi kasa a gwiwa ba, inda suka ce “Mun yi hakuri ba don son ranmu ba muka shiga yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin mu da Sheriff sakamakon kokarin wasu iyayen jam’iyya. Dama can mun sani cewa sheriff da mukarrbansa musamman Cairo Ojuogbo ba mutane bane masu mutunci ba,don haka za zasu taba rike alkawari ba

“Amma muka daure don kada a zarge mu da rashin da’a, amma tunda ba zasu canja halayyarsu ba, ta tabbata babu wata yarjejeniya da zata kawo sulhu a tsakanin mu. Barazanar dayake yi ma ma’aikatan mu ba komai bane illa barazana daga mayaudari wanda baya bin doka.

“Muna sanar da Sheriff da mutanensa dasu sani mun shigar da kara gaban kotun koli, don haka kwamitin riko na PDP na nan har sai munji daga kotu, tun da dai ba zasu iya fahimtar karamin abu ba. Idan kotun daukaka karat a sallami gwamna daga kan kujerarsa bayan yaci zabe, shin sauka yake daga kujerar ko har sai kotun koli ta yanke hukunci?"

Daga karshe yace yayan kwamitin riko na PDP karkashin jagorancin Makarfi sunyi bakin kokarinsu wajen ganin an hukunta Sheriff saboda saba yarjejeniyar da aka yi da shi, amam basu samu damar cimma ma shugaban kwmaitin sulhun ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel