Masu gurin takaran shugaban kasa a APC a zaben 2019 sun saka mi ido – Inji El-Rufai

Masu gurin takaran shugaban kasa a APC a zaben 2019 sun saka mi ido – Inji El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa masu gurinn takara shugaban kasan a cikin jam’iyyar APC sun saka masa ido saboda sun zan ya na tare da shugaba Buhari.

Malam Nasir El-Rufai ya ce, masu gurin takaran shugaban kasa a APC a zaben 2019 sun saka masa ido.

Gwamnan jihar Kaduna tare da manyan ma'aikatan gwamnatin jihar

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana wa tawagar editocin Jaridar Daily Trust, a wata hira inda ya zargi wasu mambobin jam’iyyar APC mai mulki da gurin takara a zaben 2019 mai zuwa da karkatar da wasikar da ya rubuta ga shugaba Muhammadu Buhari don cimma wata muradi.

Ya ce: "Wannan shi ne wani wasika daga gwamnan jam’iyyar APC zuwa shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC mai mulki, menene abin azo a gani? Amma ko da yake jam’iyyar adawa PDP ke munafuncin shiga tsakani na da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da suke kokarin bayyana wa shugaban ni waye. Mutanen na neman samu abin sukar gwamnatin APC. Bayan haka, akwai wasu daga cikin jam’iyyar mu APC wadanda ke gurin takara a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa 2019, sun yi imani cewa shugaba Buhari ba zai kai labari ba. Wadannan mutanen za su iya karkata abin da na rubuta wa shugaba Buhari”.

“Na yi imani da cewa ni aka nufa, wannan ba shi ne faro ba saboda ayyukana na shaida wa masu gurin takara shugabanci cewa ina tare da shugaba Buhari daram dam, kuma zan iya ba da misalai a cikin makonni biyu da ta gabata. Muddin shugaba Buhari ya nuna shawar shiga takara a zabe mai zuwa, babu shaka zan kasance tare da shi.''

KU KARANTA KUMA: Abunda na rubuta gaskiya ne, babu wanda ke bina bashi – El-Rufai

Gwamnan ya ce ba shi da abokai daga cikin waɗanda suke da gurin takara shugaban kasa. Wannan shi ne abin da ke faruwa tsakanina da su. Ina da jerin misalai dayawa a kan wannan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel