“Saura kiris Najeriya ta zama tarihi a doron kasa da ba don zuwan Buhari ba” – Gwamna Yahaya Bello

“Saura kiris Najeriya ta zama tarihi a doron kasa da ba don zuwan Buhari ba” – Gwamna Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana cewar da ba don Allah ya kawo shugaban kasa Muhamamdu Buhari ba a 2015, da Najeriya ta zaman tarihi a doron kasa.

“Saura kiris Najeriya ta zama tarihi a doron kasa da ba don zuwan Buhari ba” – Gwamna Yahaya Bello

Gwamna Yahaya Bello

Gwamnan ya bayyana haka ne a garin Lokoja yayin dayake yi ma yan jaridu bayani dangane da halin da kasa ke ciki, inda yace babu yadda za’a Najeriya ta samu galaba akan matsalar Boko Haram da cin hanci da rashawa da ba don Allah ya kawo shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

KU KARANTA: Rotsi! Jami'in hanya ya lakaɗa ma Fasto ɗan banzan duka a Zamfara, kalli yadda suka dambace

“Da Najeriya ta shiga cikin jerin kasashen da suka kasa, da bamu samu Buhari a matsayin shugaban kasa ba. Buhari ya kawo daidaito ba karami ba ga kasar Najeriya. Ba zamu manta yadda cin hanci da rashawa ya dabaibaye kasar nan ba, har ya kusan karya kasar gabaki daya ba."

Gwamnan ya kara da cewa zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa sojojin Najeriya kwarin gwiwar samun galaba da nasarori daban daban akan yan ta’addan Boko Haram.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel